Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-05-01 21:39:22    
Sauraran kide-kiden gargajiya na kasar Sin a gidan ajiye kayayyakin gargajiya na Henan

cri

A birnin Zhengzhou, babban birnin lardin Henan da ke tsakiyar kasar Sin, akwai wani gidan ajiye kayayyakin gargajiya na musamman, dukkan mutanen da suka kai ziyara a nan suna samun damar sauraran kide-kide na musamman, wadanda aka samar da su ta hanyar yin amfani da kayayyakin kida da magabatanmu suka taba yin amfani da su yau da dubban shekaru da suka wuce. Sunan wannan gidan ajiye kayayyakin gargajiya shi ne gidan ajiye kayayyakin gargajiya na Henan

Masu sauraro, abin da kuke saurara shi ne kidan da aka yi amfani da shi don maraba da baki yau da shekaru fiye da dubu 3 da suka wuce. Masu yin wasa da kayan kida na kungiyar kide-kiden gargajiya ta kasar Sin su kan fito da wannan tsohon kida don maraba da masu yawon shakatawa na gida da na ketare. Gidan ajiye kayayyakin gargajiya na Henan shi ne babban gidan ajiye kayayyakin gargajiya da aka nuna kayayyakin da ke da nasaba da tarihi da fasaha, fadinsa ya kai murabba'in mita dubu 100 ko fiye. Ya fara karbar masu yawon shakatawa a hukunce a shekarar 1998, yawan mutanen da suka kai masa ziyara ya kai dubu 300 ko fiye a ko wace shekara. Yawan kayayyakin gargajiya da ake nunawa a nan ya kai misalin dubu 130, wanda ya kai kashi daya cikin kashi takwas bisa jimlar kayayyakin gargajiya da ake nunawa a gidajen ajiye kayayyakin gargajiya a duk kasar Sin. Wasu tsoffin kayayyakin kida da aka tono ba kawai sifofinsu da danyun kayayyakin kera kayan kida sun sha bamban da na saura ba, har ma sun iya samar da kide-kide masu dadin ji, sun nuna kyakkaywar fasahar kide-kiden zamanin da na kasar Sin.

Kayan kida mafi tsoho da ake amfani da shi a cikin kungiyar kide-kiden gargajiya ta kasar Sin tarihinsa ya kai shekaru misalin dubu 8, mafi samartaka kuma tarihinsa ya kai shekaru misalin dubu 2 da dari 3. Ko da yake kide-kiden da masu gaba da mu suka taba saurara nan da dubban shekaru da suka shige suna da dadin ji, amma a zarihi kuma da wuya ne aka yi wasa da wadannan tsoffin kayayyakin kida.

1 2