Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-27 14:12:15    
An yi bikin kaddamar da wutar yula da kuma hanyar gudun yada kanin wani na mikar wutar yula ta wasannin Olympic na Beijing

cri

Mr. Jacque Rogge, shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa shi ma ya yi jawabi a gun bikin, cewa: " Na yi farin ciki matuka da ganin, cewa hanyar gudun yada kanin wani na mika wutar yula za ta ratsa ta hanyar siliki dake da ma'anar tarihi wadda kuma ta alamanta wata hanyar cinikayya da ta hada kasar Sin da sauran kasashen duniya a can can zamanin da; ban da wannan kuma za a bai wa juna wutar yula ta Olympic a wasu wuraren da ba a taba yin haka ba a da".

Jama'a masu sauraro, ko kuna sane da, cewa cibiyar kirkire-kirkire da kasafi ta kamfanin Lenovo ita ce ta yi tsarin sigar wutar yula. Wata jami'ar kamfanin Mr. Qiu Jiayu ya yi farin ciki da fadin cewa: " Abin da muka fi tunawa lokacin da muke yin tsarin sigar wutar yula, shi ne wane abu ne zai iya bayyana wata ma'ana mafi muhimmanci na tarihi. A lokacin, mun tuna da manyan kirkire-kirkire guda hudu. To, takarda daga cikinsu ta kasance wani abu ne dake bayyana kyakkyawan wayin kai. Sanin kowa ne, wayin kai na duk duniya bai taba samun sabon ci gaba ba sai dai da aka samu fasahar yin takarda. Ko shakka babu, siffar wutar yula mai kama da nadaddiyar takarda ta dace da makasudin harkar gudun yada kanin wani na mika ta, wadda kowa da kowa na iya halarta.

Ana kiran harkar nan a kan cewa " Rangadin jituwa", wadda kuma za ta iya cimma cikakkiyar nasara. ( Sani Wang )


1 2