Jiya da dare, a ginin cibiyar sabon karni dake nan birnin Beijing, an yi gagarumin bikin kaddamar da wutar yula da kuma hanyar gudun yada kanin wani na bai wa juna wutar yula da za a bi domin taron wasannin Olympic na Beijing a shekarar 2008, wanda yake janyo hankulan mutanen duk duniya.
Aminai 'yan Afrika, ko kuna sane da cewa, tun bayan da gudanar da harkar bai wa juna wutar yula a karo na farko a gun taron wasannin Olympic na Berlin a shekarar 1936, harkar mika wutar yula ta rigaya ta taka mihimmiyar rawa wajen yayata al'adun Olympic a matsayin wata harka da mutane masu yawa ke halarta, ta kuma kasance wani muhimmin kashi na tarurukan wasannin Olympic da aka gudanar a da. A gun bikin kaddamar da wutar yula da kuma hanyar da za a bi wajen gudun yada kanin wani na mika wutar yula da aka gudanar jiya da dare, Madam Chen Zhili, wakiliyar majalisar gudanarwa ta kasar Sin da Mr. Hein Verbruggen, shugaban kwamitin sulhunta harkokin taron wasannin Olympic na Beijing a karkashin tutar kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa sun cire kyallen wutar yula ta wasannin Olympic na Beijing tare; Daga baya, zaunannen mamban ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar Kwaminis ta Sin Mr. Luo Gan da shugaban kwamitin wasannin Olympic na kasa da kasa sun yi shelar hanyar da za a bi wajen gudun yada kanin wani na mika wutar yula. Za a gudanar da wannan harka ne a fadin duk duniya, wato ke nan tun daga watan Maris na shekara mai zuwa, za a soma gudun yada kanin wani na mika wutar yula daga nan Beijing zuwa birane 22 na ketare da kuma birane da yankuna 113 na cikin yankin kasar Sin.
Kuma a ran 8 ga watan Agusta da dare wato a lokacin bude taron wasannin Olympic, za a dawo da wutar yula cikin babban fili na gudanar da bikin bude taron wasannin Olympic na Beijing. An kiyasta, cewa za a dauki kwanaki 130 wajen gudun yada kanin wani na mika wutar yula a kan hanya mai tsawon kilo-mita 130,000. Shugaban kwamitin shirya taron wasannin Olympic na Beijing Mr. Liu Qi ya yi jawabi a gun bikin, inda ya furta cewa: " Wannan dai, wata harkar bai wa juna wutar yula ce da za a fi samun yawan mutane wajen gudanar da ita kan hanya mafi tsawo dake wurare mafi fadi a tarihin wasannin Olympic na zamani. Muna fatan harkar yada kanin wani na mika wutar yula ta taron wasannin Olympic na Beijing za ta sake yayata ra'ayin Olympic zuwa duk duniya da kuma bayyana zafin nama sosai da jama'ar kasar Sin suka nuna don ingiza wasannin Olympic; A lokaci daya kuma, za ta iya gwada kyakkyawar fuska da al'adun gargajiya da kuma halayyar jama'a na biranen kasashe daban-daban da wutar yula za ta ratsa, da kara samun fahimtar juna da dankon zumunci tsakanin jama'ar kasashe daban-daban; dadin dadawa, za ta iya kara yada babban take a kan cewa 'Duniya daya kuma buri daya' na taron wasannin Olympic na Beijing.
1 2
|