Malam Fan Jianchuan shi ne ya shirya da kuma kafa gidajen ajiye kayayyakin gargajiya na Jianchuan, kayayyaki da yawa da ke cikin gidajen ajiye kayayyakin gargajiyan shi ne ya yi shekaru 20 ko fiye yana tattara su da kansa. Ya san tarihin ko wanensu sosai. A wani bangare, yana yi wa wakilinmu karin bayani, a wani fanni daban kuma, yana wasa da wata babbar wuka, wadda ta riga ta yi tsatsa, ya ce, 'Mun sami wannan babbar wuka ce a lardin Shanxi, mun taba zuwa can don samun manyan wukaken da tsoffafi suka taba yin amfani da su.'
Ban da tattara kayayyakin gargajiya daga wurare daban daban, kayayyakin gargajiya da ke cikin dakunan ajiye kayayyakin gargajiya na Jianchuan suna kunshe da wadanda bakin kasashen waje suka bayar tamkar abubuwan kyauta. Wata ma'aikaciyar gidajen ajiye kayayyakin gargjiya wai ita Chen Ye ta gaya mana cewa, 'A watan Agusta na shekara ta 2005 da ta wuce, Mr. Robert Gruber, wani tsohon soja na rundunar sojojin jiragen sama na kasar Amurka mai suna 'Flying Tigers' ya kai ziyara a birnin Chengdu, ya kuma ziyarci gidajen ajiye kayayyakin gargajiyarmu, ya ba mu kayayyaki da yawa tamkar abubuwan kyauta, wadanda ya taba yin amfani da su a lokacin da yake bai wa kasar Sin tallafi a matsayin wani sojan jirgin sama a cikin yakin duniya na 2. Da zarar shigowarsa cikin dakunan ajiye kayayyakin gargajiyanmu, sai ya fara kuka, ya kuma gano wani abokin arzikinsa a kan hotunan da ke kan bango.'
Don kara nuna wa masu yawon shakatawa kayayyakin gargajiya yadda ya kamata, dakunan ajiye kayayyakin gargajiya na Jianchuan sun yi dabara a fannin sabunta hanyoyin nuni. Yanzu masu yawon shakatawa suna iya fahimtar tarihin wadannan kayayyakin gargajiya ta hanyar kallon wani tsohon fim ko wani fim din na katun, har ma ta hanyar yin wasa da wasannin video games.
Ban da yin amfani da hanyoyin kimiyya da fasaha, gidajen ajiye kayayyakin gargajiya na Jianchuan na iya bayyana harkokin tarihi ta hanyar gine-ginensu. Yawancin gine-gine a nan kwararru masu zanen gine-gine na gida da na waje su ne suka shirya su a tsanake, shi ya sa wadannan gine-gine sun nuna sigogin musamman.
Bayan kallon kayayyakin gargajiya iri daban daban, masu yawon shakatawa sun iya dan hutu a otel-otel a nan. A cikinsu kuma, otel din na Jingui ya fi nuna sigar musamman. An gina shi bisa salon tsoffin gine-gine na kasar Sin, amma an fi mai da hankali kan yin ado a ciki. Ko a cikin dakunan cin abinci, ko a cikin dakunan kwana, masu yawon shakatawa suna iya ganin yadda ake ado da kayayyakin gargajiya a ko ina a cikin wannan otel.
A shekarar nan da muke ciki, za a kara bude dakunan nuni ga masu yawon shakatawa na gida da na waje a cikin gidajen ajiye kayayyakin gargajiya na Jianchuan.
Madam Luo Yuanhui darektar otel din Jingui ta ce, 'Idan mutane sun zo nan, za su fahimci cewa, otel-otel da gidajen ajiye kayayyakin gargajiya namu sun fi kyau a duk kasar Sin, ban da kara fahimtarsu kan kasar Sin, a sa'i daya kuma, za su kara sanin al'adun kasar Sin, za su san cewa, kasar Sin wata kasa ce mai girma.' 1 2
|