Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-24 21:16:32    
Kai ziyara ga dakunan ajiye kayayyakin gargajiya na Jianchuan

cri

A garin Anren na gundumar Dayi ta lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, akwai dakunan ajiye kayayyakin gargajiya mafiya girma a duk kasar Sin, wato dakunan ajiye kayayyakin gargajiya na Jianchuan, wadanda ba na gwamnatin ba ne.

An bude wadannan dakunan ajiye kayayyakin gargajiya a watan Agusta na shekara ta 2005 da ta gabata, a wancan shekara, masu yawon shakatawa fiye da dubu 100 sun taba kai ziyara a nan. An yi shirin gina dakunan nune-nune 25 da filayen tunawa 3 da kuma otel-otel da dama, ta haka an sami babban yanki, inda aka fi samun dakunan nune-nune. Yanzu dakunan nuni 8 da filayen tunawa 2 sun fara karbar masu yawon shakatawa.

Kayayyakin da aka nuna a cikin dakunan ajiye kayayyakin gargajiya na Jianchuan ya zarce miliyan 2. Bisa ire-irensu da tarihinsu, ana nuna su bisa manyan batutuwa 3. Da farko, ana nuna kayayyakin tunawa da aka tara daga fagen daga na kasar Sin a lokacin yakin duniya na 2, wadanda suka hada da makamai da tufafi da takardu da wasiku da hotuna da dai sauransu na lokacin can. Na biyu, ana nuna kayayyakin karau da tambari da manyan hotuna da sauran kayayyakin fasaha, wadanda aka taba yin amfani da su a tsakanin shekara ta 1966 zuwa ta 1976, wani lokacin musamman na kasar Sin. Na uku kuma, ana nuna kayayyakin fasaha da ke da nasaba da al'adun gargajiya na kasar Sin, a ciki har da tsoffin kayayyakin daki da kuma hotunan da aka dauka a zamanin da da dai makamantansu.

1 2