Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-19 16:01:31    
Mr Wen Jiabao, firyin minista na kasar Sin

cri

Mr Wen Jiabao dan kabilar Han ne aka haife shi a watan Satumba na shekara ta 1942 a birnin Tianjin,a watan Afril na shekara ta 1965 ne ya shiga jam'iyyar kwaminis ta Sin,ya fara aiki a watan Satumba na shekara ta 1967 bayan da ya kammala karatunsa a jami'ar koyon ilimin geology a kan fannin geological structure,bayan karatunsa na jami'a ya cigaba da karo iliminsa daga baya ya zama injiniya.

Daga shekara ta 1960 zuwa shekara ta 1965,ya yi karatu a sashen safiyon kasa da samo ma'adinai na jami'ar geology ta birnin Beijing.Daga shekara ta 1965 zuwa shekara ta 1968,ya yi nazarin ilimin geological structure a jami'ar koyon ilimin geology ta birnin Beijing.Daga shekara ta 1968 zuwa shekara ta 1978 ya kasance mallamin fasahohi kuma mai kula da harkokin siyasa da mai azzima na sashen harkokin siyasa na kungiyar kula da ilimin geomechanics ta hukumar geology ta lardin Gansu.Daga shekara ta 1978 zuwa shekara ta 1979,shi manba ne na zaunannen kwamiti na jam'iyyar kuma mataimakin shugaban kungiyar nazarin ilimin geomechanics ta lardin Gansu.Daga shekara ta 1979 zuwa shekara ta 1981,shi mataimakin darekta na sashe kuma injiniya na hukumaar nazarin ilimin geology ta lardin Gansu,daga shekara ta 1981 zuwa shekara ta 1982,shi mataimakin shugaba ne na hukumar geology ta lalrdin Gansu.


1 2