Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-17 17:33:37    
Shelar Mr Sadr game da janye jiki daga gwamnati za ta sa Mr Maliki fuskantar babban kalubale

cri

Da farko, in ana son sake farfado da tattalin arziki da zaman rayuwar kasar Iraq, to ba za a iya rage tabbacin da aka kawo wajen tsaron kai da kyau ba. Rukunin Sadr ya janye jiki daga gwamnati, kuma ya mai da hankalin mutane a kan babban batun shirye-shiryen janyewar sojojin Amurka, wannan ya bayyana cewa, mai yiyuwa ne kungiyar masu akidar Shi'a kuma masu tsatsauren ra'ayi za su sake tayar da tashe-tashen yin sabon karfin tuwo ta yadda halin tsaron kai da ake ciki a kasar Iraq zai fuskanci babban kalubale.Tun daga tsakiyar watan Maris da sojojin Amurka da sojojin gwamnatin kasar Iraq suka tayar da ayyukan kai farmaki mai tsanani da ke da lakabi haka: dokokin shari'a da odar har zuwa yanzu, Mr Sadr ya yi ta neman wadanda ke bin sawunsa da su yi aiki ba tare da tayar da hankali sosai ba.

Na biyu, Mr Sadr yana da babban tasiri ga rukunin akidar Shi'a wanda ke samun yawancin mutanen kasar Iraq, rasa goyon baya daga Mr Sadr, tasirin Maliki wajen siyasa zai ragu. Wannan ba ma kawai saboda rukunin Sadr ya taba nuna goyon baya mai muhimmanci ga Maliki ba, hatta ma saboda rukunin Sadr yana da kujeru 30 a cikin kujeru 275 na majalisar dokoki ta Iraq , zai iya ci gaba da matsa wa gwamnatin Maliki lamba a kan batun shirye-shiryen janyewar sojojin kasar Amurka daga kasar Iraq. Shugaba Nassar Al-Rubaie na rukunin nan da ke cikin Majalisar dokoki ya bayyana cewa, zai ba da babban taimako wajen sa kaimi ga majalisar dokoki don tsara shirye-shiryen janyewar sojoji, za a kuma tsara shirye-shiryen janyewar sojoji a cikin Majalisar dokoki. Batun shirye-shiryen janyewar sojojin kasar Amurka babban batu ne wajen siyasa da tsaron kai. Kafin makon da ya wuce, Mr Sadr ya riga ya sami nasarar shirya mutane fiye da dubu goma don yin zanga-zanga a birane masu tsarki na manyan rukunonin Shi'a biyu, inda aka kirayi a tsara shirye-shiryen janyewar sojoji. Idan Mr Maliki zai ci gaba da bin sawun gwamnatin W.Bush a kan batun janyewar sojojin kasar Amurka, kuma bai ba da gudumuwa ga farfado da tattalin arziki da zaman rayuwar jama'a ba, to tabbas ne zai zama kadaici wajen siyasa.(Halima)


1 2