Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-17 17:33:37    
Shelar Mr Sadr game da janye jiki daga gwamnati za ta sa Mr Maliki fuskantar babban kalubale

cri

A ranar 16 ga wannan wata, rukunin da ke karkashin shugabancin Mr Muqtada Al-Sadr, shugaban rukuni mai akidar shi'a na kasar Iraq ya yi shelar janye jiki daga gwamnati don kai kara ga firayim ministan kasar Nuri Al- Maliki saboda ya ki neman kasar Amurka da ta tsara shirye-shiryen janye sojoji daga kasar da kuma kai kara ga sojojin Amurka saboda sun kama dakarun rundunar sojojin Mahdi da ke karkashin shugabancin Mr Sadr.

A wannan rana a birnin Bagdaza, a gun taron ganawa da manema labaru, shugaban rukunin Mr Sadr da ke Majalisar dokoki Mr Nassar Al-Rubaie ya karanta wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, ministocin da ke cikin rukunin Sadr za su janye jikinsu daga gwamnati, dayake ba a cika kujeru guda 6 bisa sanadiyar janyewar wadannan ministoci , shi ya sa ya kamata gwamnati za ta cika wadannan kujeru 6 ga mutane masu zaman kansu wadanda za su iya wakiltar burin jama'a.

A lokacin da firayim minista Maliki ya nuna maraba da janyewar ministocin rukunin Sadr daga gwamnati, ya bayyana cewa, za a cika kujeru 6 na ministoci da za a rage bisa sanadiyar janyewar rukunin Sadr daga gwamnati ta hanyar yin amfani da wadanda suka kubutar da kansu daga rikicin addinai kuma ke da kwarewa sosai wajen aiki. A cikin sanarwar da ya bayar a ranar 16 ga wannan wata, ya bayyana cewa, rarraba kujerun gwamnati bisa rukuni-rukuni na addinai ba zai iya taimaka wa kasar Iraq wajen cin nasarar yaki da wahaloli ba. Muddin dukkan kungiyoyin siyasa na kasar Iraq su yi kokari tare, to za a iya cin burin da muka ambata a baya. A cikin sanarwar, ya ci gaba da kin tsara shirye-shiryen janyewar sojojin kasar Amurka daga kasar, ya ce, batun janyewar sojoji kawance da ke girke a kasar Iraq yana jibintar da karfin da rundunar sojoji ta kasar Iraq suke da shi , wato ko zai iya sarrafa halin tsaron kai da larduna daban daban na kasar suke ciki ko a'a.

Manazartan al'amarin sun bayyana cewa, kodayake janyewar ministocin rukunin Sadr guda 6 daga ministoci 37 ba zai rusa gwamnatin Maliki ba, amma ko shakka babu abin nan da rukunin Sadr ya yi zai kawo babban cikas ga gwamnatin Maliki ta yadda za ta gamu da babban kalubale.


1 2