Tun daga shekarun 1990, kasar Sin ta fara yin bincike a kan kafa tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar manoma masu fama da talauci. Kuma an fara aiwatar da tsarin a karshen shekarar 1996. Ya zuwa yanzu, ana aiwatar da tsarin nan ne a larduna da jihohi 25. Yawan manoma da ke cin gajiyar tsarin nan ya wuce miliyan 15.
A kwanakin baya, yayin da firayim ministan kasar Sin Wen Jiabao ke gabatar da rahoto kan ayyukan gwamnati a gun taron shekarar nan na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, ya nuna cewa, a shekarar nan, za a aiwatar da tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar nanoma masu fama da talauci a duk kauyukanta. Ya ce, "ya kamata, a kafa tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar manoma masu fama da talauci a duk kauyukan kasar Sin a bana. Wannan wani babban mataki ne da aka dauka don kara kokarin raya aikin noma da kauyuka da kuma manoma, ta yadda za a raya zaman rayuwa mai jituwa a kasar."
Amma ana shan wahalhalu wajen aiwatar da tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar manoma masu fama da talauci a duk kauyukan kasar Sin, sabo da yawan manoman nan ya wuce miliyan 10 a kasar. (Halilu) 1 2
|