A cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, kasar Sin ta fara aiwatar da tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar manoma bisa gwaji a wasu kauyukan larduna da jihohi na kasar, don ba da agaji ga masu ciwo da nakasassu da tsoffafi da iyalai marasa 'yan kwadago da jama'a matalauta wadanda ke zama a kauyuka masu lalacewar yanayi da sauransu, ta yadda za su sami isasshen abinci da sutura. Tun daga shekarar nan, za a aiwatar da tsarin nan a duk kayukan kasar Sin.
Manomiya Wang Dianying mai shekaru 48 da haihuwa a bana tana daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar manoma masu fama da talauci da ake aiwatarwa a kasar Sin. Tana zama a wani kauye mai suna Xiabao na birnin Benxi na lardin Liaoning da ke a arewa maso gabashin kasar Sin. Mijinta ba ya iya yin aiki, sabo da yana fama da cututtukan amosanin gabobi da na tarin fuka da sauransu, haka kuma 'ya'yansu biyu suna karatu a makaranta. Lalle suna fama da talauci sosai. Bayan da karamar hukumar kauyensu ta sami labarinsu, sai ta shiga da iyalin manomiyar cikin sunayen manoma da take ba su kudin taimako don ba da tabbaci ga zaman rayuwarsu. Yanzu, iyalinta ya kan iya samun taimakon kudin Sin Yuan 90 daga hukumar a ko wane wata, ta haka an sassauta wahalhalu da iyalinta ke sha. Manomiya Wang Dianying ta bayyana cewa, "a da iyalinmu suna shan wahalhalu kwarai, wani sa'i ma ba mu da kudin sayen gishiri da man girke da sauran kayayyakin masarufi. Iirn wannan kudin agaji da muke samu daga hukumar ta cece mu. Yanzu, muna iya kashe kudin nan wajen samun magani domin mijina, in ba haka ba, da mijina tuni ya riga mu gidan gaskiya."
An ruwaito cewa, yawan iyalan manoma masu fama da talauci daidai kamar iyalin manomiya Wang Dianying wadanda ke samun irin wannan kudin taimako ya wuce 3,000 a lardin Liaoning na kasar Sin.
Daidai kamar lardin Liaoning, ana aiwatar da tsarin ba da tabbaci ga zaman rayuwar manoma masu fama da talauci bisa gwaji a lardin Jiangxi da ke a gabas maso tsakiyar kasar Sin. Manomi He Donghua wanda shekarunsa sun kai 35 da haihuwa a bana, yana zama a wani kauye mai suna "Huashan" na lardin Jiangxi, shi nakasasshe ne, yana fama da talauci kwarai. Ya bayyana cewa, ko da yake kudin taimako da iyalinsa ke samu daga hukumar bisa tsarin kadan ne, amma ya nuna kulawa sosai da hukumar ke yi wa manoma masu fama da talauci. Yanzu, ya bude wani kantin sayar da kayayyaki bisa kudin da ya haya. Ya ce, " a da, a ganina, ba a nuna adalci sosai a duniya, amma hukumar tana nuna mini kulawa sosai, don haka na karfafa zuciyata wajen zaman rayuwa."
1 2
|