Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-13 18:37:00    
An kaddamar da bikin shekarar musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Sin da Japan

cri

A cikin jawabinsa, Mr. Abe ya yi bayanin cewa,'Shekarar nan shekara ce ta cikon shekaru 35 da komar da huldar dake tsakanin Japan da Sin yadda ya kamata. Don tunawa da wannan muhimmiyar rana, mun mayar da wannan shekara a matsayin bikin shekarar musayar al'adu da wasannin motsa jiki. Na kan ce, kamata ya yi Japan da Sin su raya huldarsu ta hanyar kara hadin kai ta fuskar siyasa da tattalin arziki, amma a gaskiya kuma, al'adu ne ya hada kasashenmu 2 tare. Ba za a fahimci juna ba sai an fahimci al'adun juna.'

Mr. Abe ya kara da cewa, ziyarar da Mr. Wen ke yi a Japan ta sanya jama'arsa su kara mai da hankulansu kan kasar Sin, suna kuma kara kyautata huldarsu. Yana fatan Japan da Sin za su bunkasa zumunci a tsakaninsu sannu a hankali, ya kuma yi fatan cewa, za a tabbatar da cin nasarar gudanar da bikin shekarar musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Japan da Sin.

A gun gaggarumin biki da aka yi a wannan rana da dare, masu fasahar gargajiya na kasar Sin sun nuna wasanni masu ban sha'awa, wadanda hukumar kula da ilmi da kimiyya da al'adu ta Majalisar Dinkin Duniya ta tanadi da yawa daga cikinsu cikin shirin kasar Sin kan abubuwan tarihi na dan Adam na baka da kuma wadanda ba kayayyaki ba. Wasannin da masu fasaha na kasar Sin suka nuna sun jawo hankulan 'yan kallo na Japan sosai.

Wasannin da masu fasaha na kasar Sin suka nuna sun burge 'yan kallo na Japan kwarai da gaske, 'yan kallon sun kara fahimtar kyakkyawan al'adun kasar Sin.

Taken wannan bikin shekarar musaya shi ne 'Muna jiran sabuwar makoma a cikin zukatanmu', ya nuna kyakkyawan burin jama'ar Sin da Japan wajen sa ran alheri domin ganin bunkasa huldar a tsakanin kasashensu 2. Musayar al'adu na amfanawa tuntubar juna a zukatan jama'ar Sin da Japan, jama'ar wadannan kasashe 2 suna jiran sabuwar makoma a zukatansu.(Tasallah)


1 2