Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-13 18:37:00    
An kaddamar da bikin shekarar musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Sin da Japan

cri

Ran 12 ga wata da dare, a dakin nuna wasannin kwaikwayo na kasar Japan da ke birnin Tokyo, hedkwatar kasasr, an yi wani biki don kaddamar da bikin shekarar musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Sin da Japan. Firayim minista Wen Jiabao na kasar Sin da ke ziyara a Japan da kuma takwaransa na Japan Shinzo Abe sun halarci wannan kasaitaccen biki tare. Shugabannin kasashen 2 da 'yan kallo fiye da dubu daya sun kalli wasanni masu ban sha'awa da masu fasaha na kasar Sin suka nuna.

A wannan rana, bayan da ya ba da jawabi a zauren majalisar dokokin Japan da shugabantar taron kaddamar da tsarin yin tattaunawa a tsakanin manyan jami'an tattalin arziki na Sin da Japan da kuma halartar liyafar kungiyoyin sada zumunci ta Japan tare da Mr. Abe, Mr. Wen da Mr. Abe sun kuma halarci bikin kaddamar da bikin shekarar musayar al'adu da wasannin motsa jiki a tsakanin Sin da Japan. A daidai lokacin cikon shekaru 35 da komar da huldarsu yadda ya kamata, gudanar da harkokin musayar al'adu da wasannin motsa jiki daban daban ta hanyar bikin shekarar musaya yana da matukar muhimmanci ga Sin da Japan duka.

A gun wannan kasaitaccen biki da kasar Sin ta shirya, firayim minista Wen ya bayyana cewa,'Sin da Japan sun yi shekaru fiye da dubu 2 suna yin mu'amalar sada zumunta a tsakaninsu, a cikin wadannan shekaru dubu 2 ko fiye, huldodin tattalin arziki da na al'adu sun hada kasashen 2 sosai da sosai. In muna cewa, jama'ar kasashenmu 2 suna cin gajiya daga wajen hadin gwiwar tattalin arziki, to, na iya cewa, suna tuntubar juna a zukatansu saboda musayar al'adu. Shi ya sa musayar al'adu da wasannin motsa jiki wata gada ce a tsakanin jama'armu wajen sada zumunta. A daidai muhimmin lokacin da Sin da Japan suke kyautata da bunkasa huldarsu, cikin sahihanci ne muke fatan za a ci cikakkiyar nasarar kaddamar da bikin shekarar musayar al'adu da wasannin motsa jiki.'

1 2