Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-10 20:48:28    
Kallon tangaran masu launuka daban daban a birnin Jieshou na lardin Anhui

cri

Masu sauraro, a tarihin kasar Sin, a matsayinsu na wani irin kayan alatu da aka baiwa jami'ai da masu kudi na zamanin da, an yi jigilar tangaran masu launuka daban daban masu yawa daga Jieshou zuwa sauran wuraren kasar Sin ta hanyar babbar korama ta kasar. A karni na 19 da ya wuce, an fara kona tangaran a kauyuka 13 da ke kewayen Jieshou, ta haka an sami shahararrun wuraren kona tangaran a lokacin can. Yanzu wadannan wuraren kona tangaran sun bace amma sunayen wadannan kauyuka 13 suna da nasaba da wuraren kona tangaran, ya zuwa yanzu ya kasance da wasu wuraren tarihi na kananan wuraren kona tangaran na lokacin can da.

Mai yiwuwa ne masu yawon shakatawa sun fi sha'awar kona tangaran da kansu. Babu wani abu da ya fi sanya mutane su ji alfahari, sai samar da tangaran da kansu.

Masu samar da tangaran na Jieshou sun kuma koyi al'adun gargajiya na wurin, sun koyi fasahar yanke takardu da ta sassaka abubuwa kan katako. Shi ya sa ko masu fasaha na gida da na waje ko kuma masu yawon shakatawa dukkansu sun nuna babban yabo kan fasahar musamman ta tangaran masu launuka na Jieshou. Madam Yan Yumin, wata masasaka ta kasar Sin ta bayyana cewa, 'Tangaran na Jieshou sun yi suna ne sosai, har ma ana sayar da su zuwa kasashen Poland da Czech da Slovakia da Hungary, mutane na wadannan kasashe Gabashin Turai suna nuna sha'awarsu sosai kan launukan tangarannmu, saboda tangarannmu ya sharaha sosai.'

A watan Disamba na shekarar 2005 da ta gabata, an tanadi fasahar tangaran masu launuka na Jieshou na Anhui cikin shirin kasar Sin kan kiyaye abubuwan tarihi na al'adu da ba su kai na a-zo-a-gani ba na rukuni na farko, don haka irin wadannan kayayyakin fasaha masu ban mamaki sun fara jawo hankulan mutane. Mutane sun fara gadon fasahar sassaka wuka da doki da mutum tare a kan tangaran daga wajen malam Lu Shanyi. Madam Zhang Xiwen ta auri dan malam Lu, ta kuma gaji fasahar malam Lu. Ta gaya wa wakilinmu cewa, masu fasahar samar da tangaran sun yi shirin sassaka labarun da ke cikin wani shahararren littafi na kasar Sin mai suna 'labarun masarautai 3 na kasar Sin' a kan tangaran masu launuka 3, sun nemi hada fasahar tangaran masu launuka daban daban na Jieshou da kuma al'adun gargajiya na kasar Sin tare, ta haka mutanen kasashen waje za su kara saninsu kan al'adun kasar Sin saboda mashahuran tangaran masu launuka daban daban na Jieshou.


1 2