Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-04-10 20:48:28    
Kallon tangaran masu launuka daban daban a birnin Jieshou na lardin Anhui

cri

A birnin Jieshou na lardin Anhui da ke tsakiyar kasar Sin, an gaji wata tsohuwar fasahar kerar tangaran daga kakanni zuwa iyaye har na tsawon shekaru misalin dubu. Tangaran masu launuka daban daban da aka kera bisa wannan fasaha ake ajiye su a cikin dakin nune-nunen kayayyakin fasaha na kasar Sin da dakin nune-nunen kayayyakin gargajiya na kasar Sin da kuma na Victoria da Albert na kasar Birtaniya. Donme tangaran masu launuka na Jieshou sun sami karbuwa haka? A cikin shirinmu na yau, za mu dan tabo magana kan wannan dalili.

An fara kona tangaran a Jieshou tun daga zamanin daular Sui da ta Tang, wato ke nan yau da shekaru misalin dubu 1 da dari 1 da suka wuce. Fuskokin tangarann na kyalli sosai, an kuma yi zane-zane a kan fuskokin ta hanyar sassaka, an sa launuka daban daban a cikin wadannan zane-zane, bayan wannan kuma, sai a kona su. Tangarann da aka sassaka wuka da doki da mutum tare a kansu sun fi shahara bisa sauran tangaran na Jieshou. An sassaka wadannan zane-zane ne tare da la'akari da labarun wasannin kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin.

Masu sauraro, abin da kuke saurara shi ne wani babi na kalmomin wasan kwaikwayo na gargajiya na kasar Sin, malam Lu Shanyi shi ne ke karanta wadannan kalmomi, shekarunsa sun kai 87 da haihuwa, shi kuma mutum ne da ya kirkiri dabarar sassaka zane-zanen wuka da doki da mutum tare a kan fuskokin tangaran. A yayin da aka sifanta wani mutum na hawan doki, a maimakon sassaka bulalar doki kawai, malam Lu ya sassaka zane-zanen wuka da doki da mutum tare a kan fuskokin tangaran, bayan da ya sa launukan ja da fari da kore a cikin zane-zanen, ya kona tangarann.

Tangarann da aka sassaka zane-zanen wuka da doki da mutum tare a fuskokinsu na da kyan gani sosai. An ce, idan an ajiye tangarann da aka cika su da ruwa a karkashin hasken rana, to, mutane da dabbobi da ke kan fuskokin tangarann suna kasancewa kamar masu rai. Dakunan nune-nunen kayayyakin gargajiya ko kuma mutanen da suka zo daga kasashen duniya fiye da 10 sun saya ko kuma nuna tangarann da malam Lu ya kera. Ya ji alfahari sosai saboda mutanen kasashen waje na sayen tangarannsa, ya ce, ''Yan kasuwa na kasashen waje su kan yi odar tangaran da na kera, balle ma 'yan uwanmu na sauran wuraren kasarmu. Dukkansu suna sha'awar tangaranna. Irin wannan hali ba a taba ga irinsa ba a duk duniya.'

1 2