Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-30 10:56:51    
Me ya sa farashin man fetur yake ta hauhawa a kasuwannin duniya

cri

Da yake huldar dake tsakanin kasar Iran da kasashen Amurka da Burtaniya da dai sauran wasu kasashen Yamma tana ta kara lalacewa, shi ya sa 'yan cinikayya suka yi shakkar cewa mai yiwuwa ne kasar Iran wadda take ita ce babbar kasa ta biyu mai arzikin man fetur dake cikin kungiyar OPEC za ta katse hanyar samar da mai ga kasashen Yamma da kuma janyo mugun tasiri ga yunkurin samar da gurbataccen man fetur ga kasuwannin duniya. Lallai wannan lamari ya haddasa hauhawar farashin man fetur na kasa da kasa cikin makon da ya gabata.

Dalili na biyu, shi ne rahotannin yanayin sama sun bayyana cewa, kila za a gamu da karin bala'o'in guguwar iska a shiyyar mashigin teku na Mexico a wannan shekara, wato ke nan wannan mugun yanayi zai janyo illa ga aikin kawo albarkar gurbataccen man fetur a wannan shiyya. A sa'I daya kuma, yawan gurbataccen man fetur da kasar Amurka ta ajiye ya ragu sosai. Wannan shi ma ya kara haddasa hauhawar farashin man fetur.

Dalili na uku, shi ne kasar Amurka za ta fi yin amfani da mai a karshen watan Mayu na yanayin zafi har bayan an kawo karshen bikin 'yan kwadago na kasar a farkon watan Satumba na wannan shekara. Amma a duk tsawon wannan lokaci, kasashen duniya suna bukatar samun man fetur mafi yawa, kuma kila za a samu wasu matsalolin ba-zata a fannin siyasa. Wadannan al'amura za su kasance dalilin da suka sa farashin mai na kasuwannin duniya ya kara hauhawa cikin gajeran lokaci na nan gaba.

Game da yanayin farashin man fetur na kasuwannin duniya a nan gaba, wasu manazarta sun bayyana ra'ayinsu, cewa ba za a yi tsammanin samun raguwar farashin mai ba nan da 'yan kwanaki masu zuwa domin muhimmiyar magana da har ila yau take tsaida manufar farashin mai ita ce dangantakar dake tsakanin kasar Iran da kasashen Yamma. Yanzu, bangarorin biyu suna zargi da juna tare da nuna tsattsauran ra'ayoyi.

A ran 28 ga wata, sabon sakatare-janar na kungiyar OPEC wato Abdulla Salem El-Badri ya fadi, cewa ko da yake farashin mai na kasuwannin duniya yana ta hauhawa sakamakon rikicin tekun Golf, amma duk da haka, ana iya cimma burin samun isashen gurbataccen man fetur a kasuwannin duniya. Don haka ne dai, kungiyar OPEC ba za ta mayar da martani kan yanayin da ake ciki yanzu a fannin farashin mai ba.

( Sani Wang )


1 2