Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-30 10:56:51    
Me ya sa farashin man fetur yake ta hauhawa a kasuwannin duniya

cri

An labarta, cewa a 'yan kwanakin baya ba da dadewa ba, farashin man fetur na kasuwannin duniya yana ta hauhawa. Alal misali: a ran 29 ga wannan wata, farashin man fetur a bakin dola 66.03 a kan kowace ganga bisa kayayyakin da aka yi odarsu da kuma samar da su a kasuwar New York, hakan ya kai matsayin koli tun bayan ran 8 ga watan Satumba na shekarar da ta gabata. Wassu manazarta sun yi nuni da, cewa lalacewar dangantakar dake tsakanin kasar Iran da kasashen Yamma da kuma sauran wasu al'amura sun kasance muhimman dalilai da suka haddasa hauhawar farashin man fetur na kasuwannin duniya.

Da farko, a ran 23 ga watan da muke ciki, kasar Iran ta tsare sojojin ruwa guda 15 na kasar Burtaniya saboda a cewar ta sun kutsa kansu cikin haddin ruwa na Iran. A nasa bangaren, firaministan Burtaniya Mr. Tony Blair ya bayyana ra'ayinsa a ran 29 ga wata, cewa gwamnatin Burtaniya tana neman gwamnatin Iran da ta saki sojojinta; A sa'I daya kuma tana shirin buka tar kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya da ya amince da wata sanarwa. Ban da wannan kuma, kwamitin sulhu na MDD ya zartar da wata sanarwa mai lamba 1747 a ran 24 ga wata, wadda ta kara kakaba wa Iran takunkumi a fannonin dake shafar shirin bunkasa makamai masu linzami. Bangaren Iran ya ce wannan kuduri da aka amince da shi ba bisa doka ba, har ya yi shelar dakatar da yin hadin gwiwa a wasu fannoni tare da hukumar makamashin nukiliya ta kasa da kasa. A lokaci daya, ana ta kara tsananta rikicin siyasa. Bayan da sojojin ruwa na Iran suka yi atisayen soji na tsawon mako daya da wani abu a haddin ruwa na tekun Golf, sai a ran 27 ga wata sojojin kasar Amurka su ma sun yi atisayen soji bisa sikeli mafi girma a wannan shiyya. Wasu manazarta sun yi hasashen, cewa ko shakka babu kasar Amurka ta dauki wannan mataki ne domin matsa wa gwamnatin Iran lamba.

1 2