Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-23 15:39:12    
'Yan kasuwa na Taiwan da yawa suna zuba jari a birnin Yantai na kasar Sin

cri

Malam Lin Gongsong, dan kasuwa na Taiwan ya kafa masana'antunsa a birnin Yantai ne bisa babban taimako da ya samu daga wajen kungiyar. Ya ce, babban dalilin da ya sa ya zuba jari a birnin Yantai shi ne domin kyawawan sharuda na birnin da kuma hidimar da kungiyar hadin kan 'yan kasuwa na Taiwan ke yi. A ganinsa, idan wani yana so ya bunkasa harkokinsa cikin dogon lokaci, to, nuna gaskiya yana da muhimmanci sosai. A wani tsawon lokaci da ya wuce, yayin da zai sayi kayayyakin aiki domin sabuwar masakar siliki da ya kafa, akwai mutane da suka shawo kansa don ya sayi tsoffafin kayayyakin aikin ta yadda zai rage yawan kudi da yake kashewa domin sabuwar masakarsa, amma shi bai yarda da haka ba. Ya ce, "alal misali, sayi wata sabuwar mota da wata tsohuwa ya sha bamban sosai. Idan wani yana tafiya a cikin mota a kauye dake da wuyar zuwa, sabuwar mota ba za ta lalace ba, amma mai yiwuwa ne, tsohuwar mota za ta iya lalacewa, to, ko da yake tsohuwar mota na da rahusa, amma a kan sha wahala daga wajenta. Daidai da wanann misali, idan wani masana'antu ya sami odar kayayyakinsa, da ya fitar da rabin yawansu, kayayyakin aikinsa suka lalace, har bai iya kammala aikin yinsu cikin lokaci ba, zai bata ran masu odar kayayyaki. Ni kuma ina son gudanar da harkokina da kyau."

Malam Wang Xiuchen, wani jami'in hukumar birnin Yantai ya bayyana cewa, jarin da 'yan kasuwa na Taiwan ke zuba yana taka muhimmiyar rawa wajen kyautata tsarin masana'antu na birnin da na lardin Shandong. Ya ce, "jarin da 'yan kasuwa na Taiwan ke zubawa yana da muhimmanci sosai ga kyautata tsarin cinikin waje na lardin Shandong da daga kashin na'urori masu aiki da wutar lantarki cikin yawan kayayyaki da lardin ke fitarwa zuwa kasashen waje.(Halilu)


1 2