Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-23 15:39:12    
'Yan kasuwa na Taiwan da yawa suna zuba jari a birnin Yantai na kasar Sin

cri

Birnin Yantai yana lardin Shandong da ke arewancin kasar Sin, a nan wuri ne mai arzikin albarkatu. 'Yan kasuwa da yawa na Taiwan na kasar sun fara zuba jari a birnin Yantai a shekarun 1980. Bisa ci gaba da birnin ke samu cikin sauri wajen yin manyan ayyuka, 'yan kasuwa na Taiwan da ke zuba jari a birnin ma sun karu sosai a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce.

Malam Jiang Zhengping yana daya daga wadannan 'yan kasuwa na Taiwan. A shekarar 2001, shi da abokansa sun zuba kudin jari na dalar Amurka miliyan 5 wajen kafa wani babban kamfanin abinci mai suna "Wanke" a birnin Yantai. Bayan haka ba da dadewa ba, wani irin romo da ake kira "Sauce" a Turance da kamfanin ke fitarwa ya fara samun karbuwa daga wajen jama'a, kuma ya yi suna a duk lardin Shandong da birnin ke ciki. Da malam Jiang Zhengping ya tabo magana a kan kyakkyawan sakamako da kamfaninsa ya samu, sai ya ce, manyan dalilai da suka sa kamfaninsa ya iya samun kyakkyawan sakamako, su ne domin kokarin da yake yi wajen gudanar da kamfanisa, da kuma taimako da ya samu daga wajen kananan hukumomi a fannoni daban daban. A shekarar 2003, ya ci zaben zaman shugaban kungiyar hadin kan 'yan kasuwa na Taiwan ta birnin Yantai. Ya taba ba da taimako ga kamfanoni da yawa na Taiwan da su zuba jari a birnin Yantai. Ya ce, "a cikin shekarun nan biyu da suka wuce, 'yan kasuwa na Taiwan da suka zuba jari a birnin Yantai sun karu sosai. 'Yan kungiyarmu ma sun karu sosai. Don haka na kan bayyana musu abubuwa a kan halin da ake ciki a birnin dangane da zuba jari. Na gaya musu ayyuka da za su zaba su zuba musu jari. Haka kuma yayin da suka gamu da wahalhalu, sai kungiyarmu za ta taimake su wajen kawar da su."


1 2