Bayan da kasar Habasha ta yi shelar fara janye sojojinta daga kasar Somaliya a ran 23 ga watan Janairo da ya wuce, halin zaman lafiya da ake ciki a wasu yankunan kasar Somaliya ciki har da Bogadishu ya kai intaha cikin sauri. Ko da yake kungiyar tarayyar kasashen Afrika ta tsaida kuduri a kan aikawa da sojojin kiyaye zaman lafiya da yawansu ya kai 8,000 zuwa kasar Somaliya, bisa izni da ta samu daga wajen kwamitin sulhu na majalisar dinkin duniya, don maye gurbin sojojin kasar Habasha, amma ta jinkirtar da girke sojojinta a kasar, sabo da rashin zaman lafiya da isasshen kudi. Ya zuwa ran 6 ga wata, sojojin kasar Uganda 300 na rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya ta kungiyar tarayyar kasashen Afrika sun sauka Mogadishu. A lokacin da ake yin bikin maraba da su a filin jirgin sama, an harba harsassai da yawa da manyan bingiyoyi a kan filin jirgin samar. A wannan rana kuma an yi kazamin yaki a birnin Mogadishu, dakaru 'yan tawaye kusan 100 sun yi amfani da rokoki da manyan bindigogi wajen yin yaki mai zafi a tsakaninsu da sojojin gwamnatin wucin gadi ta kasar Somaliya da sojojin kasar Habasha. A ran 7 ga wata da dare, wani ayarin manyan motoci na rundunar sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar kasashen Afrika sun gamu da farmaki da dakaru wadanba ba a san su wane ne ba suka kai musu, fararen hula 9 sun rasa rayukansu yayin da bangarorin nan ke musayar wuta a tsakaninsu. Sa'an nan kuma mutane 22 ciki har da sojojin kiyaye zaman lafiya biyu sun jikkata. Bisa labarin da aka samu daga asibitocin birnin, an ce, a kalla mutane 42 sun rasa rayukansu a sakamakon yakin da aka yi a ran 13 ga wata, yawancinsu kuma yara ne.
Kafofin watsa labaru sun nuna cewa, a ran 12 ga wata, majalisar dokoki ta kasar Somaliya ta zartas da kuduri kan mayar da gwamantin wucin gadi zuwa Mogadishu ne, don kara share fage da kyau wajen yin taron sulhuntawa na duk kasar, da nuna wa jama'ar kasa da ta gamayyar kasa da kasa niyyar tabbatar da zaman lafiya a kasar yadda ya kamata. Amma abubuwa da suka faru sun nuna cewa, niyyar da aka dau ba ta isa ba, sai da tsaurarran matakai da bangarori da abin ya shafa su dauka, za a iya hana dakaru su cim ma nufinsu na tada zaune tsaye, da kuma kara shawo kan al'amuran birnin Mogadishu yadda ya kamata. (Halilu) 1 2
|