Ran 13 ga wata, a birnin Mogadishu, hedkwatar kasar Somaliya, an kai farmaki a kan Yusufu, shugaban gwamnatin wucin gadi ta kasar Somaliya. Ko da ya ke shugaba Yusufu ya tsira da ransa daga farmakin, amma halin zaman lafiya da ake ciki a birnin Mogadishu ya sake tada hankulan mutane sosai, sabo da al'amarin ya auku ne, yayin da majalisar dokoki ta kasar ta tsai da kuduri a kan mayar da gwamnatin wucin gadi ta kasar zuwa Mogadishu, babban birnin kasar.
A wannan rana da safe, shugaba Yusufu ya isa Mogadishu daga garin Baidoa a kudancin kasar inda gwamnatin wucin gadi take, kuma ba tare da bayar da sanarwa ba kafin zuwansa. Bayan saukarsa cikin wasu sa'o'i, sai aka harba harsassai guda 6 da manyan bindigogi a kan fadar shugaban kasar da ke a kudancin birnin Mogadishu. Wadanda suka shaida abin da ya faru a idanunsu, sun ce, daga cikin harsassan nan, akwai 2 wadanda suka fada a cikin farfajiyar fadar shugaban kasa, wani daban kuma da aka harba a kan wani gidan da ke daura da fadar, sakamakon haka, wani yaro mai shekaru 12 da haihuwa ya rasa ransa, yayin da wasu 3 sun jikkata. Kafin aukuwar al'amarin, an taba kai farmaki da bomb a kan ayarin motoci na wani mataimakin magajin gari na Mogadishu, inda mutane biyu suka mutu, yayin da wannan mataimakin magajin gari da sauran mutane 4 suka ji raunuka.
A ran 12 ga wata, majalisar dokoki ta kasar Somaliya ta tsai da kuduri a kan yi kaurar da gwamnatin wucin gadi ta kasar zuwa Mogadishu daga Baidoa. Bisa shirin da aka yi, wasu ministocin majalisar ministoci za su fara aikinsu a birnin Mogadishu a makon gobe. A zahiri dai, makasudin farmako da dakaru 'yan tawaye suka tayar shi ne domin hana aiwatar da kudurin.
1 2
|