Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-14 08:24:41    
Birnin Beijing yana yin kokarin kyautata aikin hidima na wasannin motsa jiki musamman domin taron wasannin Olimpic

cri

Domin kara karfafa sha`awar mazauna birnin Beijing kan wasannin motsa jiki,birnin Beijing zai shirya manyan gasannin duniya 10 kamarsu wasan kwallon rugby da na kwallon kafa da na kwallon billiards da na kwallon tennis da sauransu.Wanda a ciki,ko shakka babu gasar kwallon kafa dake tsakanin kungiyar Barcelona da kungiyar Guo`an ta Beijing ta fi jawo hankulan masu sha`awar wasan kwallon kafa na Beijing.Game da wannan,shugaba Sun Kanglin ya ce,  `Kwanan baya,na komo kasar Sin daga Barcelona,na yi shawarari da club na kwallon kafa na Barcelona kuma mun kulla wata yarjejeniya,inda aka tanada cewa,ran 3 ko ran 5 ga watan Agusta na bana,kungiyar kwallon kafa ta Barcelona za ta zo nan birnin Beijing domin yin gasa da kungiyar Guo`an ta Beijing,kila ne za a yi gasar a filin wasan ma`aikata na Beijing.`

Kazalika,don kara karfafa ilmin wasannin motsa jiki na mazauna birnin,za a kafa wani dandali domin gabatar da izni ga mazauna birnin da su yi cudanya da gogaggun `yan wasa.Kan wannan,shugaba Sun Kanglin y ace,  `Daga watan Yuli na bana,za mu gabatar da izni ga mazauna birnin musamman daliban makarantun midil da na firamare da su je sansanin `yan wasa domin kallon wasanni da gasannin da suke yi.Wasu shahararrun `yan wasa kamarsu zakarar wasan kwallon tebur ta taron wasannin Olimpic Zhang Yining da zakaran wasan kwallon boli na taron wasannin Olimpic Feng Kun da sauransu za su yi hira kai tsaye da dalibai.Aikin nan ba ma kawai zai kara yada halin jarumtaka na `yan wasa ba,har ma zai koyar da mazauna birnin wasu fasahohin wasannin,daga baya kuma wasannin motsa jiki na yin takara da na jama`a za su samu ci gaba tare.`

Ban da wannan kuma,mun samu labari cewa,don kara kyautata sharudan motsa jikin mazauna birnin,ana yin aikin share fage domin gabatar da wani irin kati ga mazauna birnin,muddin dai mazauna birnin Beijing su ajiye kudi kadan a cikin katin,to,za su iya shiga dukkan kulob-kulob a duk fadin birnin Beijing domin motsa jiki kamar yadda suke so.

To,jama`a masu sauraro,karshen shirinmu na yau ke nan,ni Jamila da na gabatar nake cewa,ku zama lafiya,sai makon gobe war haka idan Allah ya kai mu.(Jamila Zhou)


1 2