Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-14 08:24:41    
Birnin Beijing yana yin kokarin kyautata aikin hidima na wasannin motsa jiki musamman domin taron wasannin Olimpic

cri

Masu sauraro,a shekara mai zuwa wato shekarar 2008,za a yi taron wasannin Olimpic a birnin Beijing,yanzu dai birnin Beijing yana yin aikin share fage.Gwamnatin birnin tana so ta yi amfani da wannan izni don kara karfafa karfin ba da hidima kan wasannin motsa jiki,haka kuma za a gabatar da hidima mai kyau ga mazauna birnin.Saboda haka,kwanakin baya,hukumar kula da wasannin motsa jiki ta birnin Beijing ta sanar da matakai a jere.A cikin shirinmu na yau,bari mu yi muku bayani kan wannan.

Ran 28 ga watan jiya,a cibiyar watsa labarai ta taron wasannin Olimpic ta Beijing,hukumar kula da wasannin motsa jiki ta birnin Beijing ta yi taron watsa labarai kan halin aikin motsa jiki da dukkan jama`ar birnin ke ciki.A gun taron da aka yi,mataimakin shugaban hukumar Sun Xuecai ya bayyana cewa,a shekarar da muke ciki,birnin Beijing zai ci gaba da samar da gine-ginen wasannin motsa jiki masu inganci ga mazauna birnin,ta yadda kuma mazauna birnin za su ji dadin da wasannin motsa jiki ke kawo musu.

A shekarar 2007,birnin Beijing zai shirya ayyukan al`adun wasannin Olimpic a jere.An kimmanta cewa,za a shirya manyan ayyukan motsa jiki da yawansu zai kai 11,wadanda a ciki,suna kumshe da gasar kwallon tebur da ta kwallon kafa da ta kwallon kwando da ta kwallon badminton da sauransu,ban da wannan kuma,za a shirya wasu ayyukan wasannin motsa jiki na gargajiyar kasar Sin,alal misali,wasan dragon da wasan damisa.Ba ma kawai mazauna birnin Beijing suna iya shiga gasannin da za a shriya ba,har ma mutanen da suka zo birnin Beijing domin neman samun aikin yi daga sauran jihohin kasar Sin da nakasassu suna iya shiga gasannin.Shugaban hukumar kula da wasannin motsa jiki ta birnin Beijing Sun Kanglin ya fayyace cewa,za a shirya wata budaddiyar gasar nune-nunen wasan kwallon tebur a filin Tian`anmen,mutanen da za su shiga gasar za su kai dubu goma.Mr.Sun ya ce,  `Za mu shirya gasar wasan kwallon tebur a filin Tian`anmen,mutane fiye da dubu goma za su shiga gasar,a da ba mu taba shirya irin wannan aiki ba,yanzu ana yin aikin share fage.`

1 2