Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-13 16:59:20    
Wurin shakatawa na gandun daji na babban dutsen Songshan na Beijing

cri

Ni'imtattun wuraren halitta sun sami rinjaye a wurin shakatawa na babban dutsen Songshan, kuma suna da sigogin musamman. Kamar yadda ya kamata ne ake kare gandun daji da ke babban dutsen Songshan, kuma ba a taba yin amfani da shi ba. Naman daji da tsire-tsire ire-ire da yawa suna zama a nan, a ciki har da ire-ire guda 15, wadanda kasar Sin take dora muhimmanci kan kiyaye su.A cikin gandun daji da ba a taba yin amfani da shi ba, mai yiwuwa ne mutane za su iya ganin wasu namun daji da tsuntsaye a ko wane lokaci, wadanda suka bullo a cikin bishiyoyi ko bakin idon ruwa ko kuma sararin sama. Wani rafi mai tsabta yana gangara daga kan babban dutsen. Dogayen itatuwa sun rufe yawancin wuraren hasken rana, kukan namun daji da karar ruwa sun yi ta fitowa a cikin gandun daji maras hargowa, mutanen su kan yin yawo a ciki, ko kusa ba su san inda suke ba, suna son fahimtar kwanciyar hankalin da ake samu a nan, wanda ya sha bamban bisa zaman rayuwar birane.

Ban da yawon shakatawa, wurin kwana da abinci su ma sun jawo hankulan masu yawon shakatawa. A lokacin da suke ziyara a wurin shakatawa na babban dutsen Songshan, idan mutane suna son yin kwana a babban dutsen, to, sun iya yin kwana a gidajen manoman wurin, sun kuma ci abincin da manoma suka saba ci, sa'an nan kuma, su kan yi ayyukan gona da manoma su kan yi, ta haka masu yawon shakatawa suna iya fahimtar zaman rayuwar manoma.

Ban da abincin da manoma suka saba ci, mutane na iya cin abinci mai sigogin musamman a wurin shakatawa na babban dutsen Songshan. Malam He, wani jami'in hukumar harkokin yawon shakatawa ta gundumar Yanqing ta Beijing, ya gaya mana cewa, 'Masu yawon shakatawa suna iya cin abinci iri daban daban masu sigogin musamman, wadanda ke da nasaba da al'adar bikin aure ta gargajiya ta wurin. An ce, dole ne a samar da abinci a cikin kwanoni manya 8 da kanana 8 a gun bikin aurar amarya, a wani lokaci ma, an samar da abinci cikin kwanoni manya 8 da kanana 6. Mun yi wasu gyare-gyare kan al'adar gargajiya, abincin da muke samarwa na dacewa da masu yawon shakatawa.'

Bayan yawo a babban gandun daji da kuma cin abinci mai dadi, yin wanka a idon ruwa mai zafi ya iya sassauta gajiyar mutane. Idon ruwa mai zafi na babban dutsen Songshan ya shahara tun can da har zuwa yanzu, ruwan na kunshe da abubuwa da yawa masu gina jiki. Yin wanka a wannan idon ruwa mai zafi kullum ba kawai ya iya sassauta matsin lambar da aka fuskanta ba, har ma ya iya shawo kan wasu cututtuka, saboda haka mutane na gida da na waje da yawa sun zo nan don yin wanka a cikin ruwa mai zafi.


1 2