Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-13 16:59:20    
Wurin shakatawa na gandun daji na babban dutsen Songshan na Beijing

cri

Abin da kuke saurara shi ne wasan gargajiya na kasar Sin, wato Kuaiban a bakin Sinawa, inda aka yi bayani kan kyawawan wurare masu ni'ima da ke wurin shakatawa na gandun daji na babban dutsen Songshan, wadda ita ce shiyyar kiyaye halitta daya tak ta kasar Sin da ke kusa da birnin Beijing. Malam Li, shugaban ofishin 'yan sanda na yankin babban dutsen Songshan da ke karkashin jagorancin hukumar tsaron lafiyar al'umma ta Beijing, shi ne ya nuna wannan wasan Kuaiban. Ya yi shekaru misalin 10 yana aiki a nan, shi mutum ne mai kishin babban dutsen Songshan ainun, in an tabo magana kan babban dutsen Songshan, to, malam Li ya kan yi magana ba tsayawa.

Ya ce, 'A takaice dai, mu kan sifanta babban dutsen Songshan da cewa, yana kasancewa da dimbin bishiyoyi da albarkatun ruwa a nan. Babban dutsen Songshan ya yi kama da inji mai samar da iskar oxygen, ana iya shakar iska mai kyau a ko ina a ko wane lokaci, wannan ya kawo babban alheri ga lafiyar mutane. Ina jin dadin zaman rayuwata a nan sosai saboda numfashin danyar iska da shan ruwa mai tsabta.'

Wurin shakatawa na gandun daji na babban dutsen Songshan yana a arewa maso yammacin gundumar Yanqing ta birnin Beijing, wanda ke da nisan kilomita 90 ko fiye a tsakaninsa da Beijing, fadinsa ya kai kadada misalin 4660, a cikinsa kuma, tsayin babban dutse na Haituo ya zama na biyu a duk birnin Beijing saboda tsayinsa ya kai misalin mita 2199 daga leburin teku. A shekara ta 1986, majalisar gudanarwa ta kasar Sin ta mayar da wurin shakatawa na gandun daji na babban dutsen Songshan tamkar shiyyar kiyaye halitta ta kasar. Bayan da mutane suka shiga cikin wannan wurin shakatawa, wanda ake kiransa 'lambun 'yan birnin Beijing', masu yawon shakatawa sun more idanunsu da tsaunuka kwarra da ruwa mai tsabta, kuma suna shakar iska mai kyau. Ana dan sanyi a babban dutsen Songshan, matsakaicin yawan zafi a nan ya kai misalin digiri 7 a duk shekara, wanda ya yi kasa da na Beijing har da digiri 4. A lokacin zafi, mutane da yawa su kan je wajen don gudun zafi.

1 2