A shekarar 1894, Mr Sun Yat-sen ya tafi zuwa birnin Beijing tare da wasu masu fasahohi don aika wa daular mulkin gargajiya ta wancan zamani wasika, inda suka yi fatan gwamnati za ta yi gayre-gyare, amma ba su cim ma burinsu ba, da ya gano babu damar samun makoma mai kyau ba, sai ya fahimci cewa, tsarin mulkin gargajiya shi ne katanga mafi girma da aka gitta ga kwaskwarimar da ake neman yi a zamantakewar al'umma, in ana son tumbuke tsarin gargajiya, to ya kamata a yi juyin juya hali bisa babban mataki. A wannan shekara, a kasar Amurka, Mr Sun Yat-sen ya soma zurga Sinawan da ke zama a kasashen ketare da su kafa kungiyar raya kasar Sin da kuma gabatar da ra'ayin tumbuke ikon sarakuna na mulkin gargajiya. Daga nan sai aka soma juyin juya hali na jarin hujja na kasar Sin a karkashin shugabancin Mr Sun Yat-Sen.
Daga shekarar 1907 zuwa 1911, Mr Sun Yat-sen ya shugabanci tawayen makamai da aka yi a wuraren da ke kudu maso yammancin kasar Sin har sau goma ko fiye, amma saboda ba su da karfi sosai, an yi watsi da su, har ma an ba da umurnin cigiyar kama shi, don haka ba abin da ya yi ba sai ya gudu zuwa kasashen waje, ya zuwa shekarar 1911, boren da aka yi da makamai a karkashin shugabancin SunYat-sen ya sami nasara, an kuma tumbuke mulkin mallakar sarakunan gargajiyar kasar Sin da kuma kawo karshen zamantakewar al'umma mai mulkin gargajiya.
Mr Sun Yat-sen ya mutu a shekarar 1925 bisa sanadiyar fama da ciwo.(Halima) 1 2 3
|