Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-07 17:10:22    
Wani mashahurin mutumin kasar Sin mai suna Sun Yat-sen

cri

Sun Yat-sen shi ne mashahurin mutumin da ya taba bayar da fiffitaciyar gudumuwa ga kasar Sin wajen kawo karshen tsarin mulkin gargajiyar kasar Sin.

A karshen karni na 19, tsarin mulkin gargajiyar kasar Sin ya yi kusancin kawo karshensa wanda aka aiwatar da shi har cikin shekaru fiye da dubu. Kasashen yamma da ke aiwatar da tsarin jarin hujja sun sami bunkasuwa da saurin gaske, kuma suna ta kara habaka ta hanyar yin amfani da kayayyakin makamai na zamani sosai , kasar Sin da ke baya baya bisa sanadiyar rashin karfi ta zama nama mai tsoka da kasashen yamma masu nuna fin karfi suke hadiyar yawu a kai, a karshe dai ta zama kasar da ke karkashin guntun mulkin mallaka da guntun mulkin gargajiya. Mr Sun Yat-sen shi ne ya yi zama a zamanin nan.


1 2 3