Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-06 21:02:22    
Titin al'adu na Liulichang na Beijing

cri

Bayan da aka yi masa kwaskwarima a farkon shekaru 1980, an sami tsarin titin Liulichang na yanzu, an fadada shi har sau biyu. An raba titin zuwa kashi 2, wato na yamma da na gabas, tsawonsu ya kai misalin mita 750, gidajen da ke bakin titin gidaje ne masu bene hawa daya ko biyu da aka gina da tubali bisa salon gine-gine na gargajiya na kasar Sin. Ana sayar da lu'ulu'u da kayayyakin fadi-ka-mutu da na katako a titin gabas, sa'an nan kuma, ana sayar da rubuce-rubuce da zane-zane da kayayyakin gargajiya a titin yamma. Masu yawon shakatawa na iya more idanunsu da kayayyakin da masu kantuna suke ajiyewa a cikin tagogin gilas na kantunansu. Ko kusa an iya gano kayayyakin zamanin dauloli daban daban na kasar Sin a nan, a ciki kuma akwai kayayyakin gargajiya masu daraja, da kuma kyawawan kayayyakin da aka kwaikwaya.

Yana kasancewa da tsoffin kantuna a kan titin Liulichang masu dogon tarihi. Kantin Rongbaozhai na daya daga cikinsu. An kafa shi a shekara ta 1672, nan da shekaru fiye da dari 3 ke nan da aka bude shi. Wannan tsohon kanti dakin nuna kayayyakin gargajiya ne da ke nuna al'adun gargajiya na kasar Sin. Kantin Rongbaozhai yana mallakar wata fasahar dab'i ta musamman, wadda shi kadai ne yake mallaka. Zane-zanen da kantin ya buga na da kyau sosai, har ma ba a iya bambanta zane-zanen jabu da na asali ba. Tsohon darektan kantin malam Hou Kai ya waiwaya cewa, 'Mashahurin mai zane na kasar Sin marigayi Qi Baishi ya taba zuwa kantinmu, an gayyace shi da ya bambanta tsakanin zanen asali da ya yi da kuma wanda muka buga, ya sha dudduba, amma ya gaza ganewa. Shi ya sa an tambayi ma'aikatanmu ta wayar tarho, inda ya ce, ya kamata a dudduba bayan wadannan zane-zane, zanen da muka buga ba da dadewa ba na da tsabta a baya, amma zanen asali na da dauda a baya, domin an sha taba shi.'

Yanzu kantin Rongbaozhai na sayar da rubuce-rubuce da zane-zane da takardun wasiku da kayayyakin fasaha da abubuwan karatu da rubutu irin na kasar Sin da sauran abubuwan al'adu na gargajiya na kasar Sin.

Titin Liulichang mai sigogin al'adun gargajiya na kasar Sin ya jawo mutane daga wurare daban daban na duniya. Sun yi yawon shakatawa a nan, sun fahimci kwanciyar hankali irin na musamman a nan. Malam Greg Leonard, wanda ya zo daga kasar Amurka, ya gaya mana cewa, ko da yake a karo na farko ne ya yi ziyara a nan, amma titin nan da ke da sigogin gargajiya na kasar Sin ya burge shi sosai. Ya ce, 'Wannan titi na da kyau sosai, dukan kantuna na da sigogin gargajiya, kayayyakin da ake sayarwa ba ma kawai suna jawo hankulan mutane ba, har ma ana sayar da su cikin adalci. Ina jin dadin yin yawon shakatawa a nan, kamar yadda nake yin yawon shakatawa a birnin Beijing, wannan shi ne karo na farko da na kai ziyara ga irin wannan wuri.'


1 2