Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-06 21:02:22    
Titin al'adu na Liulichang na Beijing

cri

Titin al'adu na Liulichang yana bayan kofar Hepingmen, wadda ke kudu maso yammacin filin Tian'anmen na Beijing, ana iya isa nan cikin mota har cikin tsawon mintoci fiye da goma daga filin Tian'anmen. Titin nan shahararren titi ne na al'adu, wanda ya yi suna saboda sayar da rubuce-rubuce da zane-zane da kayayyakin gargajiya. Malam Zhen Wen ya yi shekaru da dama yana zama a kan wannan titi, ya gaya mana tarihin titin al'adu na Liulichang. Ya bayyana cewa, 'Zuriyoyi masu gaba da mu suna zaune a kan wannan titi. An ce, a zamanin da, gwamnti ta kafa wurin gasa tubali don samar da Liuli wato rufin kwano da ake kira coloured glaze a Turance a nan, a farkon zamanin daular Qing, an mai da dakin gasa Liuli zuwa yammacin birnin Beijing, sannu a hankali masu sayar da littattafai da rubuce-rubuce da zane-zane suka sami rinjaye a kan wannan titi.'

A karni na 17, saboda cinikin Liuli ya sami koma baya, shi ya sa hukumar daular Qing ta shirya shagalin wasan fitilu a titin Liulichang, a sakamakon haka, an sake samun wadata a nan, a duk lokacin da ake shirya shagalin wasan fitilu, rububin mutane suna kaiwa da dawowa a kan titin.

Ban da wannan kuma, saboda titin Liulichang na kusa da fadar sarakunan kasar Sin, shi ya sa mutanen da suka zo nan Beijing don shiga jarrabawar kasa su kan taru a kansa. Wadannan mutane suna da al'adar zuwa kasuwar sayar da littattafai, saboda haka, 'yan kasuwa masu hikima sun soma sayar da littattafai a nan, sun kuma sayar da kayayyakin gargajiya da abubuwan karatu da na rutubu iri-iri 4 na gargajiya na kasar Sin wato buroshin zane da tawadar dutse da ta tsinke da kuma takarda da zane-zane.

1 2