Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-02 17:37:17    
Ana kokarin tallafa wa matalauta ta hanyar zamani bisa gwaji a lardin Qinghai na kasar Sin

cri

Daga taswira, za a gano cewa, yawancin kauyuka masu talauci da matalauta na lardin Qinghai suna zama ne kan manyan duwatsu masu wuyar zuwa. Manoman kauyukan sun dade suna aikin noma ta hanyar gargajiya don ciyar da kansu. A da, ko da yake matalauta sun iya samun abinci da suke bukata bisa agaji da kanannan hukumomi ke ba su, amma ba a iya kubutar da su daga talauci ba. Da ganin haka, a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, gwamnatin lardin Qinghai ta canja hanyar da take bi wajen tallafa wa matalauta, ta fara bunkasa harkokin sana'o'i masu rinjaye da ake iya yi a wadannan wurare, don samar wa matalauta aikin yi ta yadda za su kara samun kudin shiga mai yawa.

A wani kauye mai suna "Wanzi" da ke karkarar birnin Xining, fadar gwamnatin lardin Qinghai, an kafa wata karamar ma'aikatar yin bargon ulu iri na salon kabilar Tibet. Malam Wei Zhanyun wanda ke kula da karamar ma'aikatar ya bayyana cewa, yawancin ma'aikata da ke aiki a ma'aikatarsa mata ne na kauyen "Wangzi". Ya kara da cewa, "yanzu, yawan ma'aikata da ke aiki a wurinsa ya kai 40, matsakaicin albashi da ko wanensu ke samu ya kai kudin Sin Renminbi Yuan 3,000 zuwa 4,000 a ko wace shekara."

Wata budurwa mai suna Tie Yuechun wadda ke da shekaru 18 da haihuwa a bana wata manomiya ce. Bayan da ta gama karatunta daga makarantar sakandare, sai ta fara koyon sana'ar sakar bargon ulu, kuma ta sami aikin yi mai gamsarwa. Ta bayyana cewa, "bayan da na shiga kos din koyon sana'ar sakar bargon ulu a cikin watanni uku, sai aka dauke ni aiki, a kan aika da ni zuwa wuraren aikin sakar bargon ulu guda 16 bisa matsayina na wata injiniya. "

Yanzu, an riga an kafa wani cikakken tsarin masana'antu kamar irin wannan karamar ma'aikata a kauyukan lardin Qinghai. Kayayyaki da suke yi, ba ma kawai ana sayar da su a gida ba, har ma ana fitarwa da su zuwa kasashen waje.

Bisa kokarin da aka yi ta yi a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, yanzu lardin Qinghai ya riga ya canja hanyar da ya taba bi wajen ba da agaji ga matalauta kawai, ya fara bin hanyar bunkasa harkokin tattalin arziki don tallafa wa matalauta. (Halilu)


1 2