Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-02 17:37:17    
Ana kokarin tallafa wa matalauta ta hanyar zamani bisa gwaji a lardin Qinghai na kasar Sin

cri

Lardin Qinghai yana kan tudun Qinghai-Tibet da ke a arewa maso yammacin kasar Sin. Ko da yake lardin Qinghai lardi ne mai arzikin albarkatun kasa, amma mutanensa ba su da yawa, kuma yana da wuyar zuwa, ya zuwa yanzu dai lardin yana baya-baya a fannin tattalin arziki, idan an kwatanta shi da wurare masu sukuni da ke bakin teku na gabashin kasar Sin, matalautansa ma sun yi yawa. A sakamakon kokarin da ya yi ta yi a cikin 'yan shekarun nan da suka wuce, a hankali-hankali, lardin ya sami wata sabuwar hanya da yake bi wajen yin aikin noma ta zamani don tallafa wa matalauta.

Tun bayan da kasar Sin ta fara aiwatar da manufar yin gyare-gyare da bude wa kaashen waje kofa a karshen shekarun 1970, an bunkasa aikin noma da tattalin arzikin kauyuka na lardin Qinghai cikin sauri, a zahiri ne aka daga matsayin zaman rayuwar manoma da makiyaya, kuma an kyautata halin da ake ciki game da talauci. Amma da yake lardin Qinghai ba ya da yanayin halitta mai kyau, bai yi manyan ayyuka masu yawa ba, kuma yana yin aikin noma ne a wani bangare kawai, ya zuwa yanzu dai manoma da makiyaya na lardin suna fama da talauci sosai. Yawan kauyukan lardin masu fama da talauci ya wuce 2,400, yawan mutanensa da ke fama da talauci ya zarce miliyan 1 da dubu 190.

Yayin da Malam Song Weizhen, mataimakin shugaban ofishin kula da harkokin tallafa wa matalauta na lardin Qinghai ya tabo magana a kan batun talauci na lardin, sai ya bayyana cewa, "wurare masu talauci suna yankuna masu nisa, kuma a barbaje suke, don haka aikin tallafa wa matalauta aiki ne mai nauyi. Kazalika yawancin matalautan 'yan kananan kabalu ne."

1 2