Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-02 10:54:48    
An yi muhimmin taki kan hanyar wanzar da zaman lafiya a Somaliya

cri

Bisa nauyin da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya danka mata ne, kungiyar tarayyar Afrika za ta tura sojoji kimanin 8,000 masu kiyaye zaman lafiya zuwa kasar Somaliya don taimaka wa gwamnatin kasar wajen kwantar da kura da kuma farfado da odar zamantakewar al'ummar kasar. Kawo yanzu dai, akwai kasashen Uganda ,da Nigeria, da Brundi, da Ghana da kuma Malavi kawai da sunka bayyana aniyarsu ta aike wa Somaliya da sojoji kimanin 4,000. Hakan ya janyo wahala ga kungiyar tarayyar Afrika wajen aiwatar da matakin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya.

Wasu manazarta sun bayyana ra'ayoyinsu, cewa ko da yake an samu muhimmin ci gaba a game da wannan magana, amma har ila yau dai ana fuskantar kalubale a fannoni da dama wajen zantar da zaman lafiya a kasar Somaliya. Maganar tsaro ita ce ta fi janyo hankulan mutane na bangarori daban-daban; kuma maganar karancin kudi tana biyo bayanta ; sai kuma maganar karancin mutane masu kiyaye zaman lafiya. Manazartan sun jaddada, cewa wajibi ne kungiyar tarayyar Afrika ta sanya kokari matuka wajen warware wadannan maganganu yayin da take gudanar da yunkurin wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya.. ( Sani Wang )


1 2