Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-03-02 10:54:48    
An yi muhimmin taki kan hanyar wanzar da zaman lafiya a Somaliya

cri

Bisa labarin da wakiliyarmu ta ruwaito mana an ce, jiya Alhamis, wani babban jami'in kasar Somaliya ya furta, cewa bisa matsayin wani kashi dake cikin rundunonin sojoji masu kiyaye zaman lafiya da kungiyar tarayyar Afrika wato AU take aike wa kasar Somaliya, wani rukunin farko na sojoji masu kiyaye zaman lafiya na kasar Uganda ya rigaya ya sauka a wannan kasa. Wadannan sojoji na kasar Uganda, sojojin kiyaye zaman lafiya na kashi na farko ne da kungiyar tarayyar Afrika ta tura. Wannan dai ya shaida, cewa al'ummar kasa da kasa sun yi wani muhimmin taki kan hanya wanzar da zaman lafiya a kasar Somaliya.

Bisa labarin da aka samo daga muhimmin garin Baidoa dake kudancin Somaliya,an ce, a wannan rana da asuba, sojoji sama da 30 ciki har da wasu hafsoshin soji sun sauka a filin jirgin sama na Baidoa cikin jirgin sama mai daukar kaya, inda suka samu kyakkyawar maraba daga jami'o'in gwamnatin wurin. Ko da yake mutane da dama da suka ganewa idannunsu lamarin ,amma kuwa bangaren Uganda ya musunta labarin. Kyaftin sojojin kasa mai suna Paddy Ankunda na Uganda kuma kakakin sojojin kiyaye zaman lafiya na kungiyar tarayyar Afrika ya bayar da labarin cewa, yanzu babu sojojin Uganda a cikin yankin Somaliya. ' Bisa shirin da aka tsara', in ji shi, ' za a jibge sojojin Uganda a Somaliya a sati mai zuwa'. Amma Mr. Ankunda bai fayyace takamaiman lokaci ba. A lokaci daya kuma, shugaba Yoweri Museveni na Uganda ya halarci bikin tura sojoji sama da 1,500 na bataliyoyi guda biyu na Uganda zuwa Somaliya don wanzar da zaman lafiya a kasar. Mr. Museveni ya yi jawabi a gun bikin, inda ya fadi, cewa sojojin Uganda sun shiga cikin yankin Somaliya ne domin taimaka wa jama'ar wannan kasa wajen sake raya kasar da kuma rundunar sojojin kasar; Sa'annan ya yi fatan kada 'yan gwagwarmayar Somaliya su hari kai kan sojojin Uganda.

Jama'a masu saurare, ko kuna sane da, cewa har kullum kasar Somaliya tana cikin halin kara-a-zube tun daga shekarar 1991, sai dai har zuwa karshen shekarar da ta shige , bisa taimakon sojojin kasar Habasha makwabtaciyarta ne, gwamnatin rikon kwarya ta Somaliya wadda ta kafu cikin shekaru biyu da 'yan watanni kawai ta karbe akasarin wuraren duk kasar ciki har da birnin Mugadisho, babban birnin kasar dake cikin hannun 'yan gwagwarmaya na addinin Islama. Amma, bayan da sojojin Habasha suka soma janye jikinsu daga wannan kasa a ran 23 ga watan Janairu na wannan shekara, sai halin tsaro na wasu wurare musamman ma a birnin Mugadisho na kasar Somaliya ya shiga intaha da sauri. Wadannan 'yan gwagwarmaya sun yi barazanar kai hari kan gwamnatin rikon kwarya da kuma kasashe kawayanta da dai sojoji masu kiyaye zaman lafiya na kasa da kasa da aka jibge a wannan kasa. Ra'ayoyin bainal jama'a sun yi hasashen, cewa daidai bisa wannan yanayin tsaro ne, bangaren Uganda ya musunta labarin cewa kashin farko na sojojin Uganda sun riga sun isa Somaliya yayin da ya ki fadin takamaiman lokacin shiga cikin kasar Somaliya da sauran sojoji masu tarin yawa na Uganda za su yi.

1 2