Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-28 21:23:57    
Abinci irin na gargajiyar kasar Sin wato Jiaozi

cri

Bayan da aka gauraya nama da ganyayen lambu da masoro da citta da man girki da sauran irinsu gu daya, sai a soma yin jiaozi, an yi sifar jiaozi bisa al'adar da ake bi, wato yawancin iyalai sun yi jiaozi bisa sifar gargajiya wato irin ta sabuwar wata. An yi aikin nan kamar haka: da farko, an sami wani guntun abun da ke kunshe da garin alkama da ruwa, an murza su don yin sifarsu kamar yadda da'ira ta ke, an sa nama da ganyayen lambu da sauran abubuwan da aka hada su gu daya, sa'anan an hada wanda aka kammala murza shi don sifarsa ta zama sifar sabon wata.

Bayan da aka kammala aikin nan, sai a soma sanya Jiaozi cikin ruwan da ke tafarfasa sosai, har zuwa lokacin da ya dafu sosai. Bayan da aka sanya Jiaozi cikin ruwan da ke tafarfasa sosai, sai a yi amfani da cokali don tuka su a cikin tukunya, don kada su nutse a tukunya, ana kan zuba ruwan sanyi a cikin tukunya har sau uku, kamar yadda aka sami alheri sau uku ke nan, in lokacin ya wuce minti goma ko 20, sai Jiaozi ya dafu, sa'anan kuma a soma cin Jiaozi mai dadin ci sosai.

Wasu mutane su kan sanya tsabar kudi ko dabino a cikin Jiaozi, don nuna fatansu na samun dukiyoyi a sabuwar shekara.

Cin Jiaozi shi ne al'adar kasar Sin, in bakin kasashen waje sun sauko kasar Sin, ya kamata su dandana Jiaozi, ana cewa, in ba su taba cin Jiaozi ba, to ba su san abubuwan kasar Sin sosai ba. A wajen mutanen kasar Sin, dukkan mutanen iyalinsu sun taru gu daya, suna dafa Jiaozi, suna murna sabuwar shekara cikin farin ciki sosai, suna taya junasu murnar sabuwar shekara da yi wa junansu fatan alheri da samun kanciyar hankali.(Halima)


1 2