Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-28 21:23:57    
Abinci irin na gargajiyar kasar Sin wato Jiaozi

cri

A yawancin wuraren kasar Sin, dole ne a ci wani abinci irin na gargajiyar kasar Sin wato Jiaozi ke nan, wannan ya riga ya zama wata al'ada ga mutanen kasar Sin.

Sifar Jiaozi tana tamkar yadda sifar sabon wata ya ke da ake yi ta hanyar yin amfani da garin alkama da ganyayen lambu da nama da gishiri da sauransu, kuma ana sanya jiaozi a cikin ruwan da ke tafarfasa sosai har zuwa lokacin da ya nuna. Dayake sifar Jiaozi ta yi kama da sifar tsohon kudin kasar Sin wanda ake kiransa da cewa "Yuanbao" cikin Sinanci, shi ya sa a cikin al'adar kasar Sin, Jiaozi yana almanta dukiyoyin da ake da su, saboda an hada da garin alkama da ruwa, kuma an yi amfani da guntayensu, an sanya nama da ganyayen lambu da sauransu a ciki, sifarsa ta yi kama da abun da'ira, shi ya sa a wajen jama'a, jiaozi yana alamanta bikin ganawa da juna. Saboda haka a kowanen bikin sabuwar shekara, ana cin Jiaozi, wannan yana kawo kyakyawan alheri ga jama'a wajen samun wadatuwa da yin bikin ganawa da juna.

A cikin al'adar kasar Sin, game da abubuwan da ake sanyawa a cikin jiaozi, da sifofinsa da yadda ake ci, dukkansu ana yi ne bisa ka'idojin musamman. Da farko, za mu yi bayani dangane da abubuwan da aka sanya a cikin Jiaozi, wasu mutane su kan sanya abubuwa na irin nama tare da ganyayen lambu da gishiri da sauransu, amma wasu mutane daban suna son sanya abubuwa irin na ganyayen lambu da gishiri da sauransu kawai ba tare da nama ba. Muhimmin aikin yin jiaozi shi ne yayyanka nama da ganyayen lambu da kuma sanya sauran abubuwa kamar su gishiri da citta da masoro da citta mai 'kwaya da man girki da dai sauran irinsu a ciki. Lokacin da ake yayyanka nama da ganyayen lambu, wuka da katakon kichin suna yin karo da juna sosai, suna fitar da sauti mai karfi sosai, wato Peng! Peng! Peng!------, mutane suna son saurarar irin sautin da ke da kara sosai cikin dogon lokaci, saboda a cikin harshen Sinanci, sautin kalmar nama shi ne "You", amma sautin kalmar ganyen Lambu shi ne cai , an hada kalmomin You da Cai, don su zama kalmomi kamar yadda "You Cai" ke nan, to, wannan ya yi kamar yadda ake cewa, " da akwai dukiyoyi ke nan" , in ana yin aikin cikin dogon lokaci, to kamar yadda ana samun dukiyoyi cikin dogon lokaci, in wani iyali yana dafa jiaozi da yawa, to wannan ya almanta cewa, iyalin yana zaman rayuwa cikin wadatuwa da faranta rai sosai.

1 2