Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-27 20:44:09    
Yi ziyara a lardin Sichuan

cri

Ruwan tabkin da ke kwarin Jiuzhaigou ya sha bamban saboda canjin lokacin shekara. A bazara, an farfado da kome da kome, kankara da kankara mai taushi sun fara narkewa, ruwa na fara gudu. A lokacin zafi, kwarin Jiuzhaigou wuri ne mafi kyau wajen gudun zafi. A lokacin kaka kuma, ruwan tabkin na da kyan gani sosai saboda bishiyoyi ja jawur da ke kewayensa, sai ka ce wani zane ne aka yi. A idon wata budurwa Yina Manhong, yar kabilar Zang da ke zama a kwarin Jiuzhaigou tun tana karama, kwarin Jiuzhaigou Aljanna ce a lokacin hunturu. Ta ce, 'Kwarin Jiuzhaigou ya fi kyan gani a lokacin hunturu, a lokacin nan ruwan ya daskare, ya zama mutum-mutumi. An rufe dukan magangarun ruwa da kankara mai zurfi. A cikin kankara kuma akwai wasu rassan bishiyoyi da sauran abubuwa, sai ka ce su ne ambers.'

Sa'an nan kuma, lardin Sichuan ya dauke idanun mutane saboda al'adun kabilu mai kyau. Ban da kabilar Han, 'yan kananan kabilu 14 suna zama a wannan lardi. Yawansu suna zama a tuddan da ke yammacin lardin da kuma karkarar da ke kudancin lardin. Hanyoyin zaman rayuwarsu masu launuka daban daban da addinansu na musamman sun jawo hankulan masu yawon shakatawa.

Nagartattun al'adun mutane da wurare masu ni'ima sun sanya masu yawon shakatawa su ji mamaki sosai. Madam Sirkka Korela, wadda ta zo daga kasar Finland, ta kai wa lardin Sichuan ziyara a karo na farko. Ta yi bayanin cewa, 'Lardin Sichuan ya fi burge ni, in an kwatanta shi da sauran wuraren kasar Sin da na taba kai ziyara. Zan gaya wa abokaina, ban da biranen Beijing da Shanghai, lardin Sichuan shi ma ya dace da yawon shakatawa sosai.'

Idan an kai wa Sichuan ziyara, kada a manta da abinci mai dadin ci, wanda babbar sigar musamma ce ta wurin. Abinci da giya da ganyayen shayi irin na Sichuan sun yi suna kwarai a kasar Sin har ma a duk duniya, kowa ya sani, Sichuan wuri ne mafi kyau a fannin cin abinci. Mutanen wurin suna kishin cin abinci, ba don rayukansu da ci gabansu kawai ba, suna more kansu da farin cikin da abinci yake kawo musu, suna jin dadin zaman rayuwarsu ta hanyar cin abinci.

Abinci mai dandano da tsoffin gine-gine da kuma al'adun tarihi su dalilai ne da suka sa mutane ba su son komawa gida. A zahiri kuma, tun can da, saboda lardin Sichuan na cikin yammacin kasar Sin, tsare-tsaren kasa a nan na da yamutsi kwarai, shi ya sa da kyar ake zuwa wurin. Amma yanzu irin wannan hali ya sami kyautatuwa, hanyoyin dogo sun hada lardin Sichuan da sauran biranen kasar Sin gaba daya, ana kuma kara shimfida hanyoyin jiragen sama a tsakanin wannan lardi da sauran wurare na gida da na waje a ko wace shekara. A sa'i daya kuma, sauran wuraren ayyukan yawon shakatawa a nan suna samun kyautatuwa. Lardin Sichuan yana jiran bakon da suka zo daga wurare daban daban na gida da na waje, zai ba su hidimomi mafi kyau.


1 2