
Lardin Sichuan na cikin mafarin kogin Yangtse a kasar Sin. Shahararren kwarin Sichuan yana gabashinsa, kuma a yammacinsa kuma tudu ne. Yanzu an riga an raya ni'imtattun wurare misalin 100 zuwa wuraren shakatawa, shugaban hukumar yawon shakatawa ta lardin Sichuan Zhang Gu ya bayyana cewa, manyan shiyyoyin yawon shakatawa 5 sun fi wakiltar wadannan wuraren shakatawa. Ya ce, 'Mun fito da manyan shiyyoyin yawon shakatawa 5, su ne babban dutse mafi muhimmanci ta fuskar yada addinin Buddha wato babban dutse na Emeishan, da katon mutum-mutumin Buddha na babban dutse na Leshan, da shiyyar yawon shakatawa na kwarin Jiuzhaigou, wadda ke kunshe da kwarin Jiuzhaigou da wurin shakatawa na Huanglong da jihar kabilun Zang da Qiang mai cin gashin kanta, da madatsar ruwa ta Dujiangyan da babban dutse na Qingchengshan, da shiyyar kiyaye dabbar Panda ta Wolong ta kasar Sin, da kuma shiyyar yawon shakatawa ta al'adun daular Shu na gargajiya ta Sanxingdui.'

A gaskiya kuma wadannan manyan shiyyoyin yawon shakatawa 5 da malam Zhang ya ambata a baya suna da sigogin musamman nasu. Al al misali, manyan duwatsun Emeishan da Leshan sun shahara ne domin al'adun addinin Buddha. Babban dutse na Qingchengshan ya yi suna ne saboda ni'imtattun wurare. Dabbobin Panda na da kyan gani a shiyyar kiyaye dabbar Panda ta Wolong. Tsoffin kayayyakin tagulla da aka tono a wurin tarihi na Sanxingdui sun nuna nagartacciyar fasahar Sinawa a fannin kera kayayyaki da tagulla. Duk da haka, masu yawon shakatawa sun fi nuna sha'awa ga ruwan tabki mai launuka daban daban a kwarin Jiuzhaigou.
1 2
|