Tsarin manufofin ba da tallafi da daftarin dokar ke neman kafawa yana kunshe da dukan manufofi a fannonin masana'antu da tattalin arziki da zuba jari da kudi da haraji da ba da rancen kudi wadanda da ke da amfani ga sa kaimin samar da aikin yi, don tabbatar da manufofin yadda ya kamata, daftarin dokar ya kuma kayyade ayyukan da kananan hukumomi za su dauka a wajen sa kaimi ga samar da aikin yi, Mr.Tian Chengping ya ce,"ya kamata hukumomin da ke sama da matakan garurruwa su tsai da kara samar da aikin yi a matsayin wani muhimmin burin da za a cimma a wajen bunkasa tattalin arziki da daidaita tsarin tattalin arziki, sa'an nan su tsara shi cikin shirin bunkasuwar tattalin arziki da zaman al'umma, su tsara shiri na dogo da na matsakacin lokaci da kuma shirin aiki na shekara shekara a wajen sa kaimi ga samar da aikin yi, bayan haka, ya kamata su ware kudade yadda ya kamata daga cikin kasafin kudi don a yi amfani da su a wajen sa kaimi ga samar da aikin yi."
A nan kasar Sin, ana kiran manoman da suka je birane don samun aikin yi "manoma 'yan kwadago", sabo da matsayinsu ya yi kasa a tsakanin al'umma tare kuma da karancin fasahohin sana'a, ba ma kawai ba su da yanayin aiki mai kyau idan an kwatanta su da 'yan kwadago da suka zo daga birane, har ma albashinsu ba shi da kyau. Mr.Gao, wanda ya zo daga wani kauyen da ke lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin, ya yi shekaru da dama yana aiki a birnin Beijing, a matsayinsa na wani magini, bai gamsu da yanayin zamansa ba, ya gaya wa wakilinmu cewa,"wannan wurin kwana na ma'aikata ba shi da dumi, akwai sanyi kwarai yayin da ake zama a ciki."
Game da irin wannan hali, daftarin dokar ya kuma kayyade cewa, manoma 'yan kwadago suna da daidaicin 'yanci da 'yan kwadago da suka zo daga birane a wajen samun aikin yi. Don kyautata fasahohinsu na sana'a, daftarin ya kuma tsai da cewa, ya kamata hukumomi na matakai daban daban su ba da jagoranci ga manoma 'yan kwadago a wajen samun horaswa, kuma a sa kaimi ga hukumomi daban daban da su horar da su, don inganta karfinsu a wajen aiki.(Lubabatu) 1 2
|