Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-26 20:12:32    
Sin ta fara kafa doka don sa kaimin samar da aikin yi

cri

A fuskantar hali mai tsanani a wajen kama aikin yi, da kuma jerin matsalolin da ya haifar, ciki har da karuwar bambancin samun kudin shiga da karuwar mutanen da ba su da aikin yi, daga yau 26 ga wata, an gabatar da daftarin dokar sa kaimi ga samar da aikin yi ga hukumar kafa dokoki ta kasar Sin, wato taron zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin, don ya yi bincike a kansa, hakan nan kuma, an kama hanyar kafa dokar. Daftarin dokar dai zai kafa wani tsarin manufofi wanda zai ba da tallafi wajen sai kaimi ga samar da aikin yi, kuma zai fi mai da hankali a kan daidaita sabanin da ke tsakanin samarwa da bukata da kuma matsalar da ke kasancewa cikin tsarin 'yan kwadago, kuma zai ba da daidaicin yanci tsakanin 'yan kwadago da suka zo daga birane da kauyuka a wajen samun aikin yi.

A nan kasar Sin, har kullum, ana daukar samar da aikin yi a matsayin wani tushe na zaman rayuwar jama'a da kuma wata muhimmiyar manufa a fuskar samun kwanciyar hankalin kasa. A cikin shekaru da dama da suka wuce, bi da bi ne gwamnatin kasar Sin ta fitar da jerin manufofin da za su sa kaimi ga samar da aikin yi, wadanda har suka kara yawan jama'ar da ke da aikin yi da sama da miliyan 100 a shekaru 15 da suka wuce, kuma suka kayyade yawan jama'ar da suka rasa aikin yi a kasa da kashi 4.3%, bayan haka, gwamnati ta kuma tsai da "samar da isassun ayyukan yi" a matsayin wani babban burin da za a cimma a wajen raya zaman al'umma mai jituwa a shekara ta 2020. Amma duk da haka, Sin kasa ce da ke da dimbin al'umma, kuma ya kasance da babban bambanci a tsakanin kauyuka da birane, tare kuma da matsalar rashin saukin sake samun aikin yi da ma'aikatan da suka rasa guraban aikinsu suke fama da su sakamakon gyare-gyaren da aka yi wa masana'antu mallakar gwamnati, duk wadannan sun haifar da hali mai tsanani a nan kasar Sin a fuskar samun aikin yi. Ministan kula da 'yan kwadago da ba da tabbaci ga zaman al'umma na kasar Sin, Mr.Tian Chengping ya bayyana a gun taron zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama'ar kasar Sin cewa,"wata muhimmiyar hanyar da muke bi a wajen kafa dokar ita ce mu bayyana manufofin gwamnati a wajen sa kaimi ga samar da aikin yi, kuma mu mayar da su domin su zama wani tsari, ta yadda za a kafa wani dadadden tsari a wajen sa kaimin samar da aikin yi. Na biyu kuwa mu mai da hankali a kan daidaita manyan matsalolin da ke kasancewa a wajen sa kaimin samar da aikin yi, daftarin dokar ya kuma tsara matakan da za a dauka a kan matsalar rashin kayyade tsarin kasuwanni da koma baya a wajen bayar da ilmin sana'a da rashin saukin samun aikin yi da wadanda suka rasa guraban aikinsu suke fama da shi."

1 2