
Bugu da kari kuma Mr. Zhang ya fayyace cewa, a yankunan Sin da aka yi gwajin aiwatar da manufofin biyu, manoma sun yi maraba sosai gare su, kuma sun fara bin manufar tsarin haihuwa bisa son ransu, har ma yawan yaran da aka haifa ya samu raguwa a wasu wurare.
Kwararrun kasar Sin a fannin kula da yawan mutane su ma sun amince da wadannan sabbin manufofi sosai, suna ganin cewa, an samu sakamako mai kyau bayan da aka aiwatar da su, wanda kuma ya alamanta sauye-sauyen hasahen Sinawa a fannin haihuwa bisa tsari. Fusofesa Luo Huasong, mataimakin shugaban cibiyar nazarin yawan mutane ta jami'ar Yunnan ta kasar Sin ya bayyana cewa,
"bayan da aka aiwatar da manufofin, yawan mutanen da aka haifa ya samu raguwa, an shawo kan yawan mutane yadda ya kamata, kuma matsakaicin yawan shekarun da ko wane mutum ya samu wajen samun ilmi ya karu. Ban da wannan kuma an samu manyan sauye-sauyen tsari da salon ayyukan haihuwa bisa tsari. A da, ana tilastawa wajen bin manufar tsarin haihuwa, amma yanzu a karkashin jagorancin moriya, an fara bin manufar tsarin haihuwa bisa son rai, ta yadda za a iya cimma burin rage yawan haihuwa."(Kande Gao) 1 2 3
|