Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-19 17:10:30    
Kasar Sin tana ba da jagoranci ga fararren hula wajen yin haihuwa bisa tsarin ta bin manufofin ba da gatanci

cri

Dalilin da ya sa Madam Luo take samun yuan 700 shi ne sabo da fara aiwatar da manufar ba da kyautar kudi a matsayin yabo ga wadanda suke yin haihuwa bisa tsari a wasu kauyukan kasar Sin a shekara ta 2004. Kuma bisa abubuwan da aka tanada a cikin manufar, an ce, game da tsoffin da shekarunsu ya zarce 60 da haihuwa, kuma suke da da ko diya guda ko 'ya'ya mata biyu, gwamnatin kasar Sin za ta ba su taimakon kudi da yawansu ya kai a kalla yuan 600 a ko wace shekara.

A kauyukan kasar Sin, sabo da babu tsarin ba da tabbaci ga zamantakewar al'umma yadda ya kamata, shi ya sa yawancin tsoffi suke bukatar taimakon kudi daga yaransu, kuma wannan shi ne wani muhimmin dadilin da ya sa suke son haifuwa yara da yawa. Amma bayan da aka aiwatar da manufar ba da kyautar kudi a matsayin yabo ga wadanda suke bin tsarin haihuwa, an rage damuwar mazaunan kauyuka bisa wani matsayi, ta yadda aka taimaka musu wajen canja ra'ayoyinsu na haihuwa.

Ban da wannan manufa, gwamnatin kasar Sin ta tafiyar da wani aiki a yammacin kasar Sin, wanda ake kiransa "rage yawan yaran da aka haifa don samun wadata cikin sauri", wato an samar da kyautar kayayyaki mafi yawa a matsayin yabo ga maza da matan da ke bin manufar yin haihuwa bisa tsari bisa son ransu a yammacin kasar Sin. A waje daya kuma, za a taimake su wajen ba su kyautar kudi don kiwon shanu da tumaki da kuma raya sauran ayyukan gona, ta yadda za a kyautata zaman rayuwarsu.

Bayan da aka aiwatar da manufar ba da kyautar kudi a matsayin yabo bisa yin haihuwa bisa tsari da kuma aikin rage yawan haihuwa don samun wadata cikin sauri, an samu sakamako mai kyau sosai. Zhang Weiqing, shugaban kwamitin kula da yawan mutane da haihuwa bisa tsari na kasar Sin ya bayyana cewa,

"bayan da aka aiwatar da irin wadannan manufofi biyu, a duk fadin kasar Sin, tsoffi miliyan 1.35 da shekarunsu ya zarce 60 da haihuwa, kuma suke bin manufar tsarin haihuwa sun samu kyautar kudi da yawansu ya kai a kalla yuan 600 a ko wace shekara. Ban da wannan kuma gidaje fiye da miliyan 3 a yammacin kasar Sin sun samu kyautar kudi sakamakon tafiyar da aikin rage yawan haihuwa don samun wadata cikin sauri."


1 2 3