Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-19 17:08:12    
Takaitaccen bayani game da kabilar Hui

cri

Bayan kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, gwamnatin kasar Sin wadda ke jagoranci a karkashin jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin kuma take girmama ikon bin addini na jama'a ta soma aiwatar da manufar girmama kananan kabilun kasar Sin, ta kafa jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta a ran 25 ga watan Oktoba na shekarar 1958. Sa'an nan kuma ta kafa shiyyar Linxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta a lardin Gansu da shiyyar Changjie ta kabilar Hui mai cin gashin kanta a jihar Xinjiang da wasu gundumomin kabilar Hui mai cin gashin kansu da wasu kananan gwamnatin kabilar Hui a kauyuka. A waje daya kuma, mutanen kabilar Hui sun fara hawa kan mukaman jami'ai a cikin gwamnatocin matakai daban-daban. Bugu da kari kuma, ana girmama al'adun kabilar Hui, mutanen kabilar sun samu izinin kafa dakunan cin abinci don musulmai da kantunan sayar da abinci da kayayyakin kabilar Hui a wuraren da 'yan kabilar suke zama. Lokacin da 'yan kabilar Hui suke taya murnar bukukuwansu na addinin Musulunci, ciki har da karamar salla da babbar salla, gwamnatin kasar Sin tana nuna musu goyon baya sosai.

Mutanen kabilar Hui sun taba samun babban sakamako kan al'adu da kimiyya da fasahohi, sun taka muhimmiyar rawa wajen raya al'adun kasar Sin gaba daya. Lokacin da kasar Sin take karkashin mulkin daular Yuan, ba ma kawai sun shigar da ilmin sararin samaniya da na likitanci da gine-gine da kide-kide a kasar Sin daga kasashen yammacin Asiya ba, har ma sun fitar da fasahohin yin takardu da kamfas da yin dynamite da kasar Sin ta kirkiro zuwa nahiyar Turai. Wani masanin kabilar Hui ne ya tsara tushen duk birnin Beijing, kuma sun kware sosai kan ilmin sararin samaniya, sun taba kirkiro injunan nazarin sararin samaniya iri iri.

Bugu da kari kuma, Zheng He, wani sanannen mai yin yawo kan teku na daular Ming ta kasar Sin, shi ma dan kabilar Hui ne. Ya taba shugabanci rukunonin jiragen ruwa zuwa kasashe 37 na Asiya da Afirka har sau 7, ciki har da kasashen gabashin Afirka.

'Yan kabilar Hui suna bin addinin Musulunci. Sakamakon haka, al'adun kasashen Larabawa da na Iran sun yi tasiri sosai ga al'adun kabilar Hui ta kasar Sin.(Sanusi Chen)


1 2