Kabilar Hui karamar kabila ce da jama'arta suke zama a wurare daban-daban a duk kasar Sin. Bisa kididdigar da aka yi a shekarar 2000, yawan mutanen kabilar Hui ya kai kusan miliyan 10. Yawancinsu suna zama a jihar Ningxia ta kabilar Hui mai cin gashin kanta da lardunan Gansu da Qinghai da Henan da Hebei da Shandong da Yunnan da Beijing.
Kabilar Hui takaitaccen suna ne na kabilar Hui Hui. A cikin tarihinta, shigowar addinin Musulunci da yaduwarsa a kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen haifar kabilar Hui.
Amma, kafin kafuwar Jamhuriyar Jama'ar Sin, kabilar Hui ba ta da mukamin siyasa, tattalin arziki da al'adunta sun samun cigaba sannu a hankali. Har ma ba a amince da kasancewar kabilar Hui ba. Ya zuwa shekarar 1949, a lardin Ningxia, inda mutanen kabilar Hui suka fi yawa, akwai cikakkiyar makarantar sakandare guda 1 da farkon makarantun sakandare guda 2 kawai, babu jami'a da kwaleji ko guda.
1 2
|