Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-15 19:43:06    
Fasahar yanka takardu da jama'ar kasar Sin ke yi da almakashi

cri

Yanka takardu da ake yi da almakashi fasahar jama'ar Sin ce. Jama'ar Sin su kan yanka zane-zanen furanni da tsuntsaye da kifaye da kananan dabbobi da jarumai da kuma sauransu na takardu. Jama'ar wurare daban daban na kasar Sin su kan yanka takardun fasaharsu ne da ke da sigogin musamman iri-iri, sabo da al'adunsu da abubuwa da suke sha'awa sun sha banban. Alal misali, mutanen arewacin kasar Sin suna sha'awar yanka zane-zanen babbar fada da tsoffin jarumai na zamanin da da sauransu na takardu. Amma mutanen kudancin kasar Sin kuma suna sha'awar yanka furanni da yara masu kiwon dabbobi da makamantansu na takardu.

A da, yayin da manoman kasar Sin ba su zuwa aikin gona a lokacin hunturu, matansu sun kan taru gu daya suna yanka takardun fasaha da almakashi. Kuma wajibi ne, ko wace yarinya ta iya yanka takardun fasahar da almakashi, sa'an nan ana mayar da kwarewarta bisa matsayin da za a duba kafin ta sami miji. Amma a sakamako ci gaba da aka samu a kasar Sin, an yi watsi da wannan al'ada. Ko da yake mutane da yawa ba su koyi fasahar yanka takardu da almakashi ba, amma duk da haka yanka takardun fasaya ya zama babbar sana'a ga wasu mutane. Ya zuwa yanzu dai, ya kasance da wurin aikin yanka takardun fasaha da almakashi da kungiyar fasahar yanka takardu da almakashi a kasar Sin, kuma a kan shirya nune-nunen takardun fasaha da aka yanka da almakashi da taron kara wa juna fasahar cikin lokaci-lokaci, ana buga littattafan fasahar da zane-zanen takardun fasaha da aka yi da almakashi da sauransu.

Yanzu, a sakamakon ci gaban zamani, ana ta habaka ire-iren zane-zanen takardun fasaha da ake yanka da almakashi. Ana amfani da fasahar wajen daukar silima da kayatar da dakalin nuna wasannin fasaha da sauransu. (Halilu)


1 2