
A lokacin bikin bazara na kasar Sin, jama'a suna da al'adar manna zane-zanen takardu da aka yanka da almakashi a wurare da yawa na kasar. Sun manna zane-zanen takardu iri daban daban a kan gilashin tagogi da kofofi da akwatunan na'urori masu aiki da kwakwalwa da sauransu, don murnar ranar bikin bazara.
Amma yau da shekaru 1,000 da suka wuce, an fi yin amfani da zane-zanen takardun fasaha da aka yanka da almakashi wajen kayatarwa. Bisa abubuwa da aka rubuta a cikin littfin tarihi, an ce, a zamanin daular Tang wato karni na 7 da na 8, matan kasar Sin sun taba yin amfani da zane-zanen takardun wajen yin ado a kawunansu, sa'an wasu mutane sun sami al'adar yanka zane-zanen malaman bude littafi na takardu da almakashi don murnar shiga yanayin bazara. Ya zuwa zamanin daular Song wato karni na 12, wasu mutane sun fara yin amfani da zane-zanen takardu da aka yanka da almakashi wajen kayatar da abubuwan kyauta da suka bai wa sauran mutane, wasu sun manna zane-zanen takardun da aka yanka da almakashi a kan kofofi da tagogi, ko sun yi amfani da su wajen kayatar da banguna da madubai da fitulun gargajiya da sauransu, kuma yanka zane-zanen takardun fasaha da almakashi ya fara zama babbar sana'a ga wasu mutane.

Da almakashi ne kawai ake amfani da shi wajen yanka zane-zanen takardun fasaha, Idan wani mutum yana son koyon fasahar yanke takardun, to, abubuwa da yake bukata su ne almakashi da takardu kawai. Amma ga masu sana'ar, suna bukatar almakashi da wuka iri daban daban, don yanka zane-zanen takardu masu sarkakiya. An iya yanka zane-zanen takarda daya ko na takardu da dama. An iya yanka zane-zanen takardu masu sauki kai tsaye da almakashi, amma idan wani ya yanka zane-zanen takardu masu sarkakiya, to, wajibi ne, da farko, ya yi kofin zane-zane da ya tsara a kan takardu, sa'an nan ya yi amfani da wukake iri-iri har sama da 10 wajen sassaka takardu, kuma ko kiris, ba zai yanka takardunsa tare da wani kuskure ba, in ba haka ba, to, takardunsa za su zama takardun banza.
1 2
|