Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-15 19:40:52    
Al'adar jama'ar Sin game da manna takardun musamman a gefunan kofa don isar da sakon fatan alheri a lokacin bikin bazara

cri

Tun can zamanin da, jama'ar Sin sun fara bin wannan al'ada ne don gudun aljanu. Ana yin wata tatsuniya cewa, ya kasance da wani dutse mai ni'ima da ke a wani wuri mai suna Donghai, bishiyoyi masu samar da 'ya'ya masu suna PEAR a Turance sun game ko ina cikin dutsen, sa'an nan akwai aljanu iri daban daban da ke zama a kan dutsen, amma idan aljanun za su fita daga dutsen, to, dole ne, sai sun bi ta wata kofa. Rassan wata babbar bishiyar mai tsayi sun yi kofar. Akwai wani zakara mai launin ruwan zinariya da ke zama a kan babbar bishiyar, duk lokacin da rana ke fitowa daga gabas, sai zakara ya fara cara, nan take, duk aljanun da suka je yawo da dare, suna komawa gidajensu a kan dutsen. Yayin da suke wucewa ta kofar, akwai mala'iku biyu wadanda wadanda ke gadin kofar, suna sanya ido a kan duk aljanun, idan wani daga cikinsu ya tada zaune tsaye, to, za su daure shi da igiyar ciyawar shinkafa, su kai shi gaban damisa don ta cinye shi. Sabo da haka duk aljanun duniya suna tsoron wadannan mala'iku biyu. Da jama'a suka ji wannan tatsuniya, sai suka yi amfani da allunan bishiyar "PRAE" biyu wadanda a jikinsu suka rubuta sunayen mala'ikun biyu, suka rataye su a gefunan kofa biyu don gudun aljanu.

Zuwan karni na 7 wato zamanin daular Tang, sai aka canja sunayen mala'ikun nan biyu da ake rubuta a kan allunan zuwa sunayen janar-janar biyu na mutane. Ashe, yayin da wani sarkin daular Tang mai suna "Li Shimin" yake mafarki, aljanu sun dame shi, har bai iya yin barci mai nauyi ba. Da ganin haka, sai janar-janar biyu kamar su Qin Shubao da Yuchi Gong wadanda suka ba da babban taimakonsu wajen kafa daular Tang a kasar Sin suka fara gadi a bakin kofar fadar sarkin rike da makamai don kora aljanu. Daga nan dai, sarkin ya yi barcinsa mai nauyi sosai. Bayan 'yan kwanaki da suka wuce, sarkin ya nuna tausayi ga wadannan janar-janar biyu, sabo da wahala da suke sha wajen gadin fadarsa, don haka ba ya so su ci gaba da yin gadin, sai ya ba da umurni aka zana hotunan wadannan janar-janar masu karfi biyu, kana aka manna hotunansu a kan kofofi don magance aljanu. Da labarin ya bazu a kasar Sin, sai jama'a suka fara manna hotunan janar-janar din biyu a kan kofofinsu, kuma suka kiransu da "mala'ikun kofa". Daga baya dai, jama'a suka canja hotunansu da suke zama sunayensu. An ce, a lokacin bikin bazara na shekarar 964, wani babban mai mulki ya rubuta wasu kalmomi a kan allunan bashiyar PEAR don isar da sakon fatan alheri. Daga nan ne jama'ar kasar Sin suka fara bin al'adar manna takardun musamman a kan gefunan kofa wadanda a jikinsu ake rubuta wasu kalmomi don isar da sakon fatan alheri a lokacin bikin bazara na ko wace shekara.

Bisa al'adar gargajiyarsu, a jajiberen ranar bikin bazara wato ranar sabuwar shekara bisa kalandar manoma ta kasar Sin, masu gida su kan manna irin wadannan takardu a kan gefunan kofofinsu don isar da sakon fatan alheri. (Halilu)


1 2