Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-15 19:40:52    
Al'adar jama'ar Sin game da manna takardun musamman a gefunan kofa don isar da sakon fatan alheri a lokacin bikin bazara

cri

Ran 18 ga wata ranar bikin bazara ce ta jama'ar kasar Sin, bikin nan kuma biki ne mafi girma gare su, wannan rana kuma ranar sabuwar shekara ce bisa kalandar gargajiya ta manoman kasar. Akwai al'adun gargajiya iri daban daban da ake bi don murnar bikin bazara a kasar Sin, manna takardun musamman a kan gefunan kofa don isar da sakon fatan laheri yana daya daga cikinsu.

A gabannin ranar bikin bazara, iyalan kasar Sin su saba da manna sabbin takardu wadanda a jikinsu ake rubuta wasu kalmomi a gefunan kofa biyu don isar da sakon fatan alheri. Takardun nan jajjaye ne, kuma kalmomi da aka rubuta a kansu bakake ne. An rubuta kalmomin ne musamman domin isar da sakon fatan alheri, kamar "yanayin bazara na karatowa, zaman alheri ga jama'a " da makamantansu.

1 2