Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-14 20:49:41    
Bikin "Laba" na gargajiyar kasar Sin

cri

An yada cewa, kafin Sykyamuni ya zama mai bautawa addinin Buddah sosai, ya sha wahalhalu da yawa, ya rame sosai da sosai saboda sakamakon fama da jin 'yunwa, shi ya sa ya yi tsammanin bari burinsa na bin addinin Buddah, a daidai wannan lokaci ne, ya yi karo da wata yarinyar da ke kiwon dabbobi, yarinyar ta mika masa wani kwanon da ke cike da tuwo, bayan da ya ci tuwon, sai ya kara kuzarinsa nan da nan, ya yi tunani sosai a karkashin wata bishiya mai suna Pipal, daga nan sai ya zama mai bautawa addinin Buddah sosai. Don tunawa da al'amarin nan, masu bin addinin Buddah sun dafa tuwo ta hanyar yin amfani da gero mai yauki tare da 'kwayoyin 'ya'yan itatuwa iri iri da yawa don nuna girmamawa ga mai bautawa addinin Buddah da kuma samar wa matalauta masu fama da 'yunwa sosai, an ce irin tuwo shi ne tuwon "Laba".

Babban abu da ake yi a bikin Laba shi ne cin tuwo na Laba. Ana bin al'adar nan ne daga wajen karni na 10. A wancan zamani, a ranar 8 ga watan Disamba, wato ranar bikin Laba, daga fadar sarakuna da gidajen manyan jami'ai zuwa dakunan ibada, dukansu suna dafa tuwo, kuma a tsakanin jama'a, kowane iyali ma ya dafa tuwo, kuma dukan mutanen iyalin sun taru gu daya don shan tuwon, an riga an yi irin al'adar har cikin shekaru dubu ko fiye. A tsakanin jama'a, an dafa tuwon Laba hada da hatsi iri iri guda 8, duk domin dace da ranar 8, hakan da aka yi shi ne don yin habaicin samun alheri. Cikin tuwon nan har da shimkafa da wake da gero da alkama da masara da dawa da dai sauransu, wasu ma an sanya gyada da dabino da busasshen 'ya'yan itatuwa a ciki, in tuwon ya dafu, sai aka sa sukari a ciki, kai tuwon ya yi dadi sosai.

A arewacin kasar Sin, mutane suna da al'adar jika tafarnuwa, uwayen gidaje suna cire bawon tafarnuwa, sun sa su a cikin kwanon da ke cike da vinegar , sa'anan kuma sun rufe bakin kwanon, kuma sun ajiye kwanon a cikin daki mai dumama. Ya zuwa daren jajibirin sabuwar shekarar yanayin bazara, to za a debe su don cinye su tare da abinci irin musamman na kasar Sin wato Jiaozi wanda aka dafa su da garin alkama da ganyayen lambu da nama da dai sauransu. Tafarnuwan da aka jika launinta ya canja, ya zama kore shar, na da kyaun gani sosai.

A zamanin yau a kasar Sin, ana ci gaba da bin al'adar yin bikin nuna girmamawa a ranar 8 ga watan disamba na kalandar noma , amma an fi shirya bikin ne a kauyuka. A birane, dimbin samari sun mayar da al'adar cin tuwon Laba tamkar yadda damar da suka samu ta yin taruwar cin abinci tare da mutanen iyalansu kawai, ba su lura da ma'anar bikin Laba ko tarihinsa ba.(Halima)


1 2