Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-14 20:49:41    
Bikin "Laba" na gargajiyar kasar Sin

cri

Ranar 26 ga watan Janairu na shekarar da muke ciki, rana ce ta 8 ga watan Disamba ta kalandar noma ta kasar Sin. A kasar Sin, watan Disamba na kalandar noma ta kasar Sin ana kiransa ne da cewa, "watan La", saboda haka ana kiran ranar 8 ga watan Disamba na kalandar noma ta kasar Sin da cewa, "Laba". Bikin "Laba" biki ne na gargajiyar kasar Sin, ana mayar da ranar a gabanin bikin yanayin bazara na gargajiyar kasar Sin, wato "Chunjie" ke nan. Yau za mu gabatar da wasu abubuwa dangane da bikin Laba.

A zamanin aru aru na kasar Sin, mutane suna bin wata al'adar gargajiya, wato yin bikin tunawa da kakani-kakaninsu a karshen shekara da kuma yin bikin girmama aljannu da dai sauran irinsu don neman alheri da kara tsawon rayuka da kuma kawar da miyagun abubuwa da karbar abubuwan alheri. An bayyana cewa, bikin nan shi ne bikin La na tunawa da abubuwa. A kai a kai ne, mutane su kan kiran karshen wata na kowace shekara , wato watan Disamba da cewar wai 'Layue", bikin "Laba" biki ne mai muhimmanci a cikin watan Disamba.

Tun daga zamanin aru aru har zuwa yanzu , kasar Sin tana mai da hankali ga sha'anin noma. A ganin mutane na zamanin aru-aru na kasar Sin, girbi mai kyau da aka samu a kullum shi ne sakamako da aka samu bisa taimakon aljannu daga sararin samaniya da kasa da dai sauransu, sai sun shirya babban bikin murnar samun girbi mai kyau, wato bikin nuna girmamawa na La. Bayan bikin, mutane suna taruwa gu daya kuma sun dafa tuwo da wani irin gero mai yauki don murnar samun girbi mai kyau. A kwana a tashi, irin bikin da aka yi ya zama bikin da iyalai daban daban suka yi don tunawa da kakani-kakaninsu. Bayan da aka shigar da addinin Buddah a kasar Sin, sai masu bin addinin Buddah suka kara wasu sabbin abubuwan da ake yi a bikin, wato a ce ranar 8 ga watan Disamba na kalantar noma ta kasar Sin rana ce da kakanin masu bin addinin Buddah Sykyamuni ya zama mai bautawa addinin Buddah sosai.

1 2