Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-12 19:15:09    
Masana'antun zirga-zirgar jirgin sama na kasar Sin sun dukufa kan yin nazari da kansa

cri

Ban da wannan kuma, kasar Sin tana nacewa ga bin ka'idar yin nazari da kirkire-kirkire cikin cin gashin kai lokacin da take kera jiragen sama na fasinja.

Geng Ruguang, mataimakin manajan kamfanin farko na masana'antun zirga-zirgar jiragen sama na kasar Sin ya bayyana cewa, a shekarar da ta gabata, an riga an fara yin gwajin kera sabon jirgin sama na fasinja mai cin gajerren zango da ake kiransa ARJ21 wanda kamfanin ya yi nazari a kai. Kuma ya ce, ba kawai akwai yalwa sosai a cikin irin wannan jirgin sama ba idan an kwatanta shi da sauran jiragen sama masu cin gajerren zango, har ma zai iya biyan sauran bukatu, alal misali, zai iya tashi da kuma sauka a filayen jirgin sama na tudun da ke yammacin kasar Sin, ban da wannan kuma zai iya tafiya a kan hanyoyi masu sarkakiya. Ya zuwa yanzu, kamfanin ya riga ya samu takartun oda 71 na sayen jirgin sama mai lamba ARJ21. Bisa shirin da aka tsara, za a kaddamar da gwajin yin amfani da wannan jirgin sama a watan Maris na shekara mai zuwa, kuma za a yi amfani da su a hukunce a shekara ta 2009.

A waje daya kuma, game da wani jirgin sama na fasinja daban mai cin gajerren zango wanda ake kiransa MA60, ya zuwa yanzu an riga an fitar da su da dimbin yawa zuwa kasashe waje. Mr. Geng ya gaya mana cewa, "a fannin masana'antun jiragen sama na fasinja, yawan takardun oda da muka samu na sayen jirgin sama mai lamba ARJ21 ya kai 71. Haka kuma a shekara ta 2006, kamfanin ya daddale yarjeniyoyi da kuma kwangila kan batun sayar da jiragen sama 62 masu lamba MA60 ga kasashen Zimbabwe da Laos da Zambia da Congo da Nepal da Indonesia da Cuba da Fiji da dai sauransu, ta haka muka cimma burinmu na fitar da jiragen sama na sari wadanda muka kera cikin cin gashin kai zuwa kasashen waje." Kande Gao)


1 2