Sin ciki da waje (chinaabc)Rediyon kasar SinSashen Hausa
China Radio International
Labarun gida
Labarun duniya
Labarun Siyasa
Labarun Tattalin Arziki
Labarun Al'adu
Labarun Wasanni
Sauran Labaru
Saurari labarai da dumi-duminsu da sauran shirye-shirye
more>>
[ Al'adu ]
 --Al'adun Sinawa
 --Kabilun kasar Sin
[ Bunkasuwa ]
 --Tattalin arziki
 --Bunkasuwar Sin
[ Yawon shakatawa ]
 --Yawo a kasar Sin
 --Wurare masu yawo
[ Ilmi, Lafiya ]
 --Fagen bincike
 --Kiwon lafiya
[ Wasanni ]
 --Labaran wasannin
 --Me ka sani
(GMT+08:00) 2007-02-12 19:15:09    
Masana'antun zirga-zirgar jirgin sama na kasar Sin sun dukufa kan yin nazari da kansa

cri

Ba da jimawa ba, an yi gwajin fada ta musamman a sararin sama na wani filin jirgin sama na kasar Sin tsakanin jiragen saman yaki biyu da kasar Sin ta kera da kanta da jiragen saman yaki hudu na makiya. A karshe dai, sabbin jiragen saman yaki da ake kiransu J10 wadanda kasar Sin ke da cikakken ikon mallakar ilminsu ya ci nasara sosai a cikin wannan rawar daji da aka yi.

Song Wencong, babban mai zayyane zayyane ne na wannan jirgin saman yaki ya gaya mana cewa, kasar Sin ta fara yin nazari da kuma kera jirgin saman yaki mai lamba J10 a shekaru 80 na karnin da ya gabata. Kuma nasarar da aka ci wajen kera shi tana daya daga cikin muhimman sakamako mai kyau da kasar Sin ta samu wajen dukufa kan samun bunkasuwa bisa kafin kanta a fannin masana'antun zirga-zirgar jirgin sama. Ta haka za a ci gaba da inganta karfin sojojin jiragen sama na kasar Sin wajen tsaron kai da yaki. Ban da wannan kuma Mr. Song ya bayyana cewa "Kera jirgin saman yaki mai lamba J10 cikin nasara ya ba da muhimmin tasiri sosai. Wato wannan ya shaida cewa, yanzu kasar Sin tana da jiragen saman yaki na zamani a duniya. Kuma dalilin da ya sa muka samu nasarar kera wannan jirgin saman yaki shi ne sabo da lokacin da muka fara yin nazari da kuma kera shi, mun riga mun tsai da kudurin kai matsayin ilmin kimiyya da fasaha na zamani na duniya."

Bisa matsayinsa na sabon jirgin saman yaki da ke da amfani da yawa, an raba jirgin saman yaki mai lamba J10 iri biyu, daya shi ne wanda ke da kujera guda, dayan kuma shi ne wanda ke da kujeru biyu. Ban da wannan kuma an fasalta su da fasahohi na zamani wajen kera su, alal misali, an hada fikafikan jirgin saman yaki da jikinsa tare lokacin da ake yin fasafinsu domin samun saukin boye jiki da kuma kara adana mai na tankin jirgin, hakan ya kyautata ingancin jirgin saman yaki.

Bisa labarin da muka samu, an ce, ya zuwa yanzu, an riga an fara yin amfani da jiragen saman yaki masu lamba J10 a cikin rundunar mayakan sama na kasar Sin. Kuma kamfanin masana'antun zirga-zirgar jirgin sama na birnin Chengdu na kasar Sin tana daukar nauyin samar da irin wannan jirgin saman yaki. Luo Ronghuai, shugaban kamfanin ya nuna cewa, nasarar da aka samu wajen kera jirgin saman yaki mai lamba J10 ba kawai sakamako mai kyau da aka samu a fannin masana'antun zirga-zirgar jirgin sama na kasar Sin ba, a'a har ma za ta sa kaimi ga bunkasuwar dukkan tsarin masana'antun kasar Sin. Kuma ya ce, "Nasarar da aka samu wajen kera jirgin saman yaki mai lamba J10 ta alamanta cewa, kasar Sin ta riga ta kafa wani tsarin masana'antu wajen yin nazari da kera jirage bisa karfin kanta a fannin masana'atun zirga-zirgar jiragen sama, wadda ta fi taka muhimmiyar rawa ga masana'antun kera jiragen sama na kasar Sin idan an kwatanta da aikin kera jirgin saman yaki mai lamba J10."

1 2